An karrama dan agajin da ya tsinci miliyan 100

Dan agajin ya tsinci sama da Naira miliyan, amma ya mika su ga ‘yan sanda domin nemo mai su.

An karrama dan agajin da ya tsinci miliyan 100

An bai wa dan agajin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS), Salihu AbdulHadi Kankia, kyautar kujerar aikin hajji sakamakon dawo da Naira miliyan 100 da ya tsinta a Jihar Bauchi.

Wannan na zuwa ne lokacin bikin rufe taron shirin tafsirin watan Ramadan na bana da malaman addinin Musulunci suka yi a Jihar  Bauchi.

Daraktan Kungiyar Agaji na kasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti ne, ya gabatar da Kankia don a yaba masa kan dawo da makudan kudin da ya yi.

A wani sako da JIBWIS reshen Jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, “Kankia ya gano wata jaka dauke da makudan kudade sama da naira miliyan 100.

“Maimakon ya tsere da kudin, sai ya garzaya ofishin ‘yan sanda inda ya mika jakar kudin, ‘yan sandan sun yi nasarar gano mai jakar, kuma sun tabbatar da babu abin da ya bata a ciki.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar Izala ta karrama shi da lambar yabo tare da biya masa kujerar aikin hajjin bana.

“Bugu da kari, dan majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Abdulmalik Zannan Bangud, ya ba shi kyautar Naira miliyan biyu.

“Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya  ba shi kyautar mota kirar bas don fara neman kudi da ita.”

NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

’Yan bindiga sun lalata tashar wutar lantarkin da ake ginawa a Kogi

Trump ya bai wa Elon Musk muƙami a Gwamnatin Amurka

Dalilin da ke haddasa yawaitar katsewar lantarki — EFCC