An karrama malama mai magana da harsuna 35
A bairnin Landan, an karrama wata malama mai suna Andria Zafirakou a matsayin malamar da ya ta fi hazaka bayan ta iya magana da harsuna 35 da dalibanta suke ji. Andria wadda ke koyarwa a makarantar Sakandaren Alperton da ke Arewa maso Yammacin Landan, ta lashe kyautar ce ta Gidauniyar barkey ta malaman duniya, kuma […]
A bairnin Landan, an karrama wata malama mai suna Andria Zafirakou a matsayin malamar da ya ta fi hazaka bayan ta iya magana da harsuna 35 da dalibanta suke ji.
Andria wadda ke koyarwa a makarantar Sakandaren Alperton da ke Arewa maso Yammacin Landan, ta lashe kyautar ce ta Gidauniyar barkey ta malaman duniya, kuma za a ba ta kyautar Fam 715,000 (sama da Naira miliyan 300).
Malamar ta samu nasarar lashe kyautar ce bayan ta taimaka wa daliban da suka fito daga daya daga cikin yankin da ke fama da rashin ci gaba a fannin ilimi da sauran ababen more rayuwa.
Daga cikin kokarin da ta yi, malamar ta koyi harsuna 35 da dalibanta suke amfani da su a makarantar, wadanda suka hada da Gujarati da Hindi da Tamil da sauransu domin ta rika tattaunawa da iyayen daliban idan sun zo makarantar.
Da take bayani a kan yadda ta ji bayan ta samu wannan nasara, malamar cewa ta yi, “Na yi mamaki matuka. Abin ya daure min kai domin ban taba tunanin cewa zan samu wannan kyautar ba.”
Ta kara da cewa dukan malaman Ingila suna da hazaka da kokari wajen koyar da dalibai abin da ya kamata, inda ta ce “Na sadaukar da wannan kyautar ga dukan malaman.”
Da aka tambaye ta ko me za ta yi da kudin, sai ta ce, “Zan bi a hankali ne. Zan zauna in yi tunani tukunna, amma kamar yadda ka sani ne, zai yi kyau sosai idan na samu damar shirya biki na musamman a cikin makarantarmu.”
Firayi Ministar Ingila, Theresa May ta taya malamar murna a wani sakon bidiyo da ta aike wanda aka nuna a wajen bikin karrama malamar a birnin Dubai.
A cewar Firayi Ministar, “Kin cancanci wannan kyautar bisa yadda kike da kokari da kirkira wajen yin aikinki. Zama malami mai inganci na bukatar dagewa da sanyin rai. Wadannan su ne wasu daga cikin halayen da kika nuna wa dalibanki. Don haka muna godiya bisa yadda kike wannan kokari, kuma muna fata za ki ci gaba.”
A shekara 12 da ta yi tana koyarwa a makarantar Alperton, malamar ta sake tsara manhajar karatun makarantar tare da taimakon sauran malamai domin ta amfani daliban yadda ya kamata, sannan ta bude wajen wasanni na mata zalla domin mata da suka fito daga kasashen masu ra’ayin rikau, kuma tana ziyartar gidajen dalibanta domin kula da rayuwarsu yadda ya kamata wani lokacin har takan shiga cikin motar daukar dalibai.
Malamar ta kara da cewa, “Wadansu daliban ba sa iya shiga cikin wasu tsare-tsaren da na shirya bayan makaranta saboda suna taya iyayensu aiki a gida kuma suna zuwa dauko kannensu a wasu makarantun. Da na lura da haka, kuma na lura cewa wadansu daga cikinsu suna samun matsala kan aikin da aka ba su a gida saboda matsatsi, sai na kara wasu ayyuka a makarantar, kuma na bude wasu ajujuwa na musamman a ranakun da babu makaranta domin daliban su samu damar yi abin da ya kamata cikin natsuwa.”
Bayan wannan kyauta da ta samu, yanzu malamar ta zama wakiliyar Gidauniyar barkey, wanda zai sa ta ci gaba da koyarwa na akalla shekara biyar masu zuwa, kuma za a biya ta kudin ne kadan- kadan.