An karrama malaman makarantar Umarabs
Malaman Makaratar Umarabs biyar ne suka amfana da kyautar albashin wata daya da kuma na’urar firiji kowannnesu sakamakon koyarwa a makarantar na tsawon shekara goma.Malaman su ne Malam Aliyu da Malam Yunusa Suleiman da Malam Nasiru Yusuf da Malama Adama Usman da Liman Malam Jamilu Yusuf, inda aka hada musu da takardun yabo daga hukumar […]
Malaman Makaratar Umarabs biyar ne suka amfana da kyautar albashin wata daya da kuma na’urar firiji kowannnesu sakamakon koyarwa a makarantar na tsawon shekara goma.
Malaman su ne Malam Aliyu da Malam Yunusa Suleiman da Malam Nasiru Yusuf da Malama Adama Usman da Liman Malam Jamilu Yusuf, inda aka hada musu da takardun yabo daga hukumar makarantar.
Da yake jawabi wajen karrama malaman a taron yayen dalibai karo na 10, Babban Daraktan Makarantan Malam Isa Sa’idu ya ce an ba malaman kyaututtukan ne saboda namijin kokari da sadaukar da kan da suka yi wajen koyar da dalibai a tsawon shekara 10 da kafa makarantar.
Malam Isa Sa’idu ya kuma jinjina musu bisa irin daurewar da suka nuna don ganin makarantar ta tsaya a kan kafafunta tun daga lokacin da aka kafa ta zuwa yau.
daliban da suka nuna bajinta a bangarori daban-daban sun samu kyaututtuka don yaba kwazonsu.
Babban bako mai jawabi, Dokta Abubakar Sa’ad na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya
ya nanata muhinmancin ba yara ilimin addini da na zamani domin su taso da kyakkyawar akida da za ta zame musu jagora a al’amuransu na rayuwa. Kuma ya ce ilimi shi ne kadai gadon da ba za iya raba mutum da shi ba, kuma gobara ba ta cinsa ’yan fashi ba sa iya sace shi, kuma tsufa bai iya nakasa shi.
Shugaban taron Alhaji Usman Suleiman ya yaba wa hukumar makarantar da daukacin malamanta bisa yadda suke zage dantse wajan ba yara ingantaccen ilimi.