An karrama matar da ta kwashe shekara 43 a matsayin namiji

A ranar Talatar makon jiya ne wata kungiya a kasar Masar ta karrama wata mata da ta shafe shekara 43 tana shigar maza saboda ta samu sukunin neman abin da za ta sanya a bakin salati.  Matar mai suna, Sisa Abu Daooh tana da shekara 64 kuma tana zaune ne a birnin Ludor na kasar, […]

An karrama matar da ta kwashe shekara 43 a matsayin namiji
An karrama matar da ta kwashe shekara 43 a matsayin namiji

A ranar Talatar makon jiya ne wata kungiya a kasar Masar ta karrama wata mata da ta shafe shekara 43 tana shigar maza saboda ta samu sukunin neman abin da za ta sanya a bakin salati. 

Matar mai suna, Sisa Abu Daooh tana da shekara 64 kuma tana zaune ne a birnin Ludor na kasar, ta kasance tana wannan badda kaman ne saboda samar wa kanta da ’ya’yanta da kuma jikokinta abin da za su ci da kuma sha. Sisa ta rasa mai gidanta ne lokacin da take dauke da juna biyu kuma bayan ta haihu sai ta fahimci cewa ba ta da wata hanyar samun kudin shiga, kamar yadda kafar yada labarai ta Al Arabiya Net ta bayyana.
Yanayin da ta samu kanta ya kara munana ne saboda wata al’ada da ke matukar adawa da aikin mata a yankin da take. Wannan ya sa take shiga irin ta maza ta nufi kauyukan da ba a santa ba sosai domin yin sana’ar da za ta dauki nauyin abin da mijinta ya bari.
Matar tana aikin yin bulo ne da goge takalma. Kuma ba ta dade da aurar da diyarta ga wani mutum wanda daga bisani ya fada rashin lafiyar da ta tilasta masa barin aiki. Hakan ya sanya ta daukar nauyin diyarta da kuma surukin nata.