An karrama sakataren labarai na Gwamnan Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karrama sakataren yada labarai na gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Mu’azu Dakin-gari tare da wadansu mutane biyar a makon da ya gabata a gidan gwamnatin Kebbi. Wadanda aka karrama din sun hada da Aliyu Galadima da Ibrahim Mode da Yusuf Usman da Faruk Umar Zaki da kuma Kabiru Dan-ruwa.An karrama su ne […]

An karrama sakataren labarai na Gwamnan Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karrama sakataren yada labarai na gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Mu’azu Dakin-gari tare da wadansu mutane biyar a makon da ya gabata a gidan gwamnatin Kebbi.

Wadanda aka karrama din sun hada da Aliyu Galadima da Ibrahim Mode da Yusuf Usman da Faruk Umar Zaki da kuma Kabiru Dan-ruwa.An karrama su ne sakamkon nuna kwazo da kuma kula da aikin Gwamnati kamar yadda dokar aikin ta tanada, wanda ofishin babban sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi ta shirya.

Jim kadan bayan mika lambobin yabon gare su, an kuma ba su kyaututtukan karfafa gwiwa inda kowa ya sami kyautar mashin guda, turamen zannuwa guda biyu da babbar riga guda-guda, domin nuna godiya gare su bisa yadda suka nuna hazaka da kuma kwazo a yayin gudanar da aikinsu.

A yayin jawabinsa, Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar Dutsin-mari ya bayyana cewa wannan karramawar da aka yi wa mutane shida, an yi ta ne bisa cancanta domin duk wanda yake aiki a gidan gwanatin Kebbi zai shaida haka akan wadannan mutane da aka karrama kan irin rawar da suke takawa akan ayyukansu. Haka zalika ya ce tun lokacin da suka fara aiki a gidan Gwamnatin Jihar Kebbi ba a taba kama su da wani laifi ko wani korafi ba.

Ya kara da cewa wannan bukin shi ne karo na biyu, kuma nan da wadansu watanni masu zuwa za a karrama wadansu ma’aikatan biisa cancanta kamar wannan. Sannan sai ya godewa dukkan ma’aikatan fadar Gwamnatin ta Kebbi akan goyon bayan da suke ba shi wajen gudanar da aikin Gwamnatin baki daya.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Abubakar Udu Idris ya bayyana jin dadinsa akan irin yadda babban sakataren fadar gidan Gwamnatin Kebbi ya ke yi karrama ma’aikatan jihar. Sai kuma ya yi kira ga sauran sakatarorin ma’aikatun Gwamnatin Jihar Kebbi da su yi koyi da takwaran nasu, Garba Umar Dutsen-mari wajen karrama ma’aikatan da suka ciri tuta wajen gudanar da ayyukansu, domin wannan ne zai kara maido da martabar aikin Gwamnati a jihar Kebbi.