An karrama Shugabar Kamfanin Kowa Group a Jami’ar ABU
A makon jiya ne aka kaddamar tare da rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Daliban Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya ’yan asalin Jihar Kaduna, (KADSSU). Dan majalisa mai wakiltar Zariya da Kewaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo ne ya jagoranci wani sashe na taron da ya samu halartar farfesoshi da manyan malamai […]
A makon jiya ne aka kaddamar tare da rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Daliban Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya ’yan asalin Jihar Kaduna, (KADSSU).
Dan majalisa mai wakiltar Zariya da Kewaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo ne ya jagoranci wani sashe na taron da ya samu halartar farfesoshi da manyan malamai daga ciki da wajen jami’ar da ’yan siyasa da sauransu.
A taron wanda ya gudana a dakin taro na jami’ar, an karrama Shugabar Kamfanonin Kowa Group of Companies kuma Shugabar Gidauniyar Center for Charity and Debelopment of Women and Children in Africa, Hajiya Binta Abdullahi Kowa da matsayin Uwar Daliban Najeriya.
Da yake jawabi, dan majalisa Suleiman Dabo ya ce Hajiya Binta ta cancanci wannan karramawar, inda ya ce an karrama ta a daidai lokacin da ya dace inda dalibai suke neman taimako daga gwamnati da kungiyoyi domin su dogara da kansu musamman a halin da muke ciki na tabarbarewar tarbiyya.
Da take jawabi Hajiya Binta Kowa ta yi godiya ga Allah da shugabannin daliban da kasa baki daya bisa zabarta da suka yi domin wannan karramawar daga cikin mata da yawa masu irin wannan ayyuka. Sannan ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da sauran gwamnatocin Arewa su mayar da hankali wajen ilimantar da kananan yara da marayu da mata domin kawar da miyagun halaye, inda ta ce rashin ilimi ne ke kawo miyagun halaye da rashin zaman lafiya. Ta ce a shirye suke su hada gwiwa da gwamnati wajen cimma wannan buri, musamman a bangaren magance matsalar barace-barace da koya wa mata da kananan yara sana’a da ba su tallafin karatu da sauransu.
Sannan a karshe ta ce duk lokacin da bukatar irin wannan ya taso, a shirye take ta yi amfani da gidauniyar domin taimakon al’umma.