An karrama Shugabar kungiyar ‘Yan Jarida saboda taimakon matasa

An karrama Hajiya Fatima Muhammad Paga a matsayin Jakadiyar Matasa saboda yadda take kokarin samar wa matsa sana’o’in da za su dogaro da kansu. Wani kamfani da ke ba da fifiko wajen kula da harkokin karatun matasa a Jihar Yobe mai suna ZUDAM ne ya karrama ta da lambar yabon ta Yobe Youth Ambassador. Da […]

An karrama Shugabar kungiyar ‘Yan Jarida saboda taimakon matasa

An karrama Hajiya Fatima Muhammad Paga a matsayin Jakadiyar Matasa saboda yadda take kokarin samar wa matsa sana’o’in da za su dogaro da kansu.

Wani kamfani da ke ba da fifiko wajen kula da harkokin karatun matasa a Jihar Yobe mai suna ZUDAM ne ya karrama ta da lambar yabon ta Yobe Youth Ambassador.

Da yake jawabi, babban jami’in gudanarwa na kamfanin Muhammad Maina Muhammad, ya ce sun lura da irin kokarin da take yi ne na bai wa matasa fifiko musamman a bangaren da ya shafi ilimi da koya musu sana’o’i don dogaro da kansu.

Muhammad Maina Muhammad, ya ce sun ba ta lambar yabon ce ta  Jakadiyar Matasa don kara mata kwarin gwiwa wajen ci gaba da tallafa wa matasa domin da za a samu mutane masu irin wannan hali nata a Jihar Yobe gwamnati ma za ta samu sauki wajen wasu aikace-aikace.

A nata tsokacin Hajiya Fatima Muhammad Paga, wacce ita ce Shugabar kungiyar Mata ’Yan Jarida ta kasa (NAWOJ) reshen Jihar Yobe, cewa ta yi ta ji dadin wannan karamci da aka yi mata duk da cewa ba shi ne irinsa na farko ba, amma tana alfahari da shi domin ya shafi taimakon matasa ne kai-tsaye.

Hajiya Fatima Paga, ta ce ta jima tana daukar dawainiyar biya wa ’ya’yan Jihar Yobe kudin makaranta a lokacin da suka samu damar shiga jami’o’i ko kwalejojin ilimi da kuma taimaka musu wajen koyon sana’ao’i inda a cewarta tana yi ne don Allah ashe wasu na lura da duk abin da take yi, shi ne yanzu kamfanin Zudam suka karrama ta.

Hajiya Fatima Paga, ta ce ta sadaukar da wannan lambar yabo ga mata da matasan Jihar Yobe saboda dominsu ne aka yi mata wannan karamci.

Fatima Muhammad Paga, ita ce ’ya ta biyu daga cikin ’ya’ya bakwai da marigayi Muhammad Paga ya haifa, kuma irin wannan halayya na taimakon al’umma da ta jima tana yi ne ya sa mutanen yankin Bade ta Yamma, Jihar Yobe suke kira gare ta da amsa kiransu a 2019 ta fito musu takarar Majalisar Jiha daga yankin Bade ta Yamma, inda suke ganin ita ce za ta cire musu kitse daga wuta.