An karya farashin takardar aure a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta zaftare kudaden da ake biya na takardun shaidar aure daga ranar 1 ga watan Yuli, 2020. Ministan Harkokin Gida Rauf Aregbesola ya ce an rage farashin ne bisa shawarwarin masu ruwa da tsaki a lokacin tarukan wayar da kai a fadin Najeriya a shekarar 2019. Kalli hotunan daurin auren dan Shaikh Ja’afar […]
Gwamnatin Najeriya ta zaftare kudaden da ake biya na takardun shaidar aure daga ranar 1 ga watan Yuli, 2020.
Ministan Harkokin Gida Rauf Aregbesola ya ce an rage farashin ne bisa shawarwarin masu ruwa da tsaki a lokacin tarukan wayar da kai a fadin Najeriya a shekarar 2019.
- Kalli hotunan daurin auren dan Shaikh Ja’afar Adam
- Matar aure ta watsa wa mijinta tafasashshen ruwa
- Wata mata ta cire wa kishiyarta kunne da cizo
Daga yanzu kudin takardar shaidar auren budurwa ya koma N6,000 a shekara, sabanin N30,000 da ake biya a wata biyu-biyu a baya, a cewar ma’aikatar, wadda ta ce biyan farko za a biya na shekaru biyar.
Kudin lasisin da wuraren ibada ke biya na bazawara kuma an rage shi daga N30,000 zuwa N5,000.
Sanarwar da Kakakin ma’aikatar, Mohammed Manga ya fitar dauke da sa hannun Babbar Sakatariya kuma Babbar Mai Kula da Harkokin Aure a Najeriya, Georgina Ehuriah, ta bayyana haka.
Ta kara da cewa an zaftare kudin auren yau da kullum daga N21,000 zuwa N15,000, aure na musamman kuma an rage shi daga N35,000 zuwa N25,000.
Daga karshe Ministan ya yi kira ga duk wadanda abun ya shafa a wuraren ibada su tabbata sun samu lasisin da ake bukata, su kuma mutane su yi amfani da damar da gwamnati ta ba su na cin ribar ragin farashin.