An karya farashin takin zamani da 50% a Gombe

Gwamnatin Gombe ta karya farashinsa da kashi 50 cikin 100 ga manoma jihar domin saukake musu tsadar kayan noma.

An karya farashin takin zamani da 50% a Gombe

Takin zamani da aka rabawa manoma

Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya kaddamar da rabon takin zamani a kan rabin farashinsa ga al’ummar jihar.

Gwamnatin Gombe ta karya farashinsa da kashi 50 cikin 100 ga manoma jihar domin saukake musu tsadar kayan noma.

Takin zamanin dai gwamantin jihar na sayarwa ne a kan N22,000.

A cewar gwamnan, kai-tsaye za a sayar wa daidaikun manoma rabin takin da gwamantin ta sayo.

Ragowar kuma za a sayar musu be ta hannun kungiyoyin manoma, inda idan suna so za su mayar wa gwamnatin kudaden idan an yi girbi.

Gwamnan ya ce hakan zai tabbatar da adalci da gaskiya wajen sayar da takin zamanin domin bunkasa harkokin noma da samun wadatar abinci a jihar.

A karshe ya yi kira da a yi zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya domin cigaban jihar.