An karyata labarin duhun duniya na kwana 15

An karyata rahoton matsanancin duhun duniya da aka gabatar wa duniya, musamman a shafukan sadarwar wasu kafafen yada labarari da Facebbok, an tabatar da cewa, duniya za ta yi fama da  duhun na tsawon makonni biyu ko kwana 15. Kuma a wata ruwayar snce duhun na kwana shidda ne, kamar yadda sahfukan labarai na Newswatch […]

An karyata labarin duhun duniya na kwana 15
An karyata labarin duhun duniya na kwana 15

An karyata rahoton matsanancin duhun duniya da aka gabatar wa duniya, musamman a shafukan sadarwar wasu kafafen yada labarari da Facebbok, an tabatar da cewa, duniya za ta yi fama da  duhun na tsawon makonni biyu ko kwana 15. Kuma a wata ruwayar snce duhun na kwana shidda ne, kamar yadda sahfukan labarai na Newswatch 33 da huzlers. Com suka watsa wa duniya.
A makon da ya wuce mun aminiya ta bayyana cewa, Charles Bolden, wani babban jami’in NASA ya gabatar da makala mai shafi dubu a fadar White House, amma daga bisani shafin sadarwa na Snope.com ya bayyana cewa, NewsWatch33 ne ke baza irin wadannan labaran, bayan an rufe shafin da ke yada jita-jita na Newswatch28 a tsakiyar shekarar nan ta 2015. Kuma shi ken an sauran masu baza jita-jita suka yada a shafukan sadarwa  na intanet. Mafi yawan labaran wadannan kafofi duk an bayyana su a matsayin barkwanci ko kuma shaci-fadi.
Shafin NewsWatch33 ya sha yada barkwanci da yaudara, musamman inda ya taba nuni da cewa, mgoya bayan wani da ya yi harbin kan mai uwa da wabi da ake kira Charleson, wanda ya yi harbin a Dylan Roof, sun tara Dala miliyan hudu, don ba shi kariyar shari’a. Kuma wutar wayar iPhone ta ja wata yarinya a kunnuwanta. Sannan mawaka Jay-Z da Beyonce, sun sayi hakkin mallakar tutar jihar Amurka mai cin gashin kanta, sannan Gwamnatin Tarayya ta sanya wa taba mai arha na’urar jin Magana. daukacin wadannan labarai da aka baje a shafukan intanet, NewsWatch33 ya yada su.
Uwa-uba, har yanzu manyan kafafen yada labarai na duniya irin su BBC da bOA da Rfi na France duk ba su yi wani dogon sharhi a kan al’amarin ba, ta yadda za a tabbatar da ingancinsa. Kafofin da suka bijiro da alamar tambaya akan kafafen yada labarai, su ne kuora.com da ibtimes.com.