An karyata mutuwar ’yar fim Angelina Okorie
A farkon makon nan ne kafafen watsa labarai suka bayyana mutuwar ’yar fim din Kudancin Najeriya, Angelina Okorie. Sai dai daga bisani aka gane cewa kuskure aka yi, domin kuwa ’yar fim din da ta mutun ba Angelinar ba ce.Kamar yadda labarin ya bazu, an nuna cewa Angelina ta mutu ne a wurin haihuwa. Jim […]

A farkon makon nan ne kafafen watsa labarai suka bayyana mutuwar ’yar fim din Kudancin Najeriya, Angelina Okorie. Sai dai daga bisani aka gane cewa kuskure aka yi, domin kuwa ’yar fim din da ta mutun ba Angelinar ba ce.
Kamar yadda labarin ya bazu, an nuna cewa Angelina ta mutu ne a wurin haihuwa. Jim kadan da jin labarin sai masoyanta suka fara rige-rigen aikawa da sakonnin ta’aziyya. Daga bisani ne aka samu tabbacin cewa ashe wata ’yar fim din ce ta mutu mai suna Ijeoma Okori.
kungiyar ’Yan Wasa Ta Najeriya (AGN), Reshen Jihar Ribas ta fitar da takardar sanarwa ga ’yan jarida mai cewa: “Muna cike da alhinin sanar da mutuwar daya daga cikin membobinmu, Misis Ijeoma Okori, wacce ke zaune a Eleme. Ta mutu ne a yayin haihuwa da safiyar Lahadi. Haka kuma, abin bakin cikin shi ne, ’yar fim din ta mutu ne tare da tagwayen ’ya’yan da ta haifa.”
Ita kuwa Angelina Okorie, tuni ta bayar da sanarwar karyata labarin mutuwar tata ta turakarta a Facebook; inda ta ce: “Ni dai ban mutu ba. A kashin gaskiya, an kara mani shekara 150 a rayuwata. Ina rokon Allah Ya jikan dukkan mutanen da suka yi amfani da hotona a turakunsu na intanet da jarida suna cewa ni Angela na mutu. Har yanzu dai ina nan cikin ganiyar rayuwata, ruhina na nan a raye. Allah ne kadai zai iya daukar raina.”
Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito, a halin yanzu dai Angelina Okorie tana kan aikin daukar sabon fim tare da mai bayar da umurni, Tchidi Chikere, a Inugu.