An kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda Junaidu Fasagora a Zamfara

Jihar Zamfara, inda a can aka kashe Junaidu Fasagora, ta yi ƙaurin suna a wajen hare-haren ’yan bindiga.

An kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda Junaidu Fasagora a Zamfara

Rundunar Sojin Nijeriya da ke yaƙi da ta’addanci a Jihar Zamfara ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan ta’adda Junaidu Fasagora.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar a ranar Laraba da daddare.

Rundunar sojin ta ce ta yi nasarar kashe Fasagora tare da mayaƙansa da dama ne bayan wani zazzafan ba-ta-kashi da aka yi a yankin Tsafe.

“Junaidu Fasagora da ƙungiyarsa ta ta’addanci sun daɗe suna addabar mutane da satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci a al’ummomin jihohi da dama a Arewa maso Yamma,” in ji rundunar.

Rundunar sojin ta ce kawar da ’yan ta’addan wata muhimmiyar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta’addanci da tayar da ƙayar baya.

“Wannan nasarar da rundunar ta samu dai wani ƙarin haske ne na yadda sojojin Najeriya ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da sauran yankunan kasar.

“Sojojin suna ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci, tada ƙayar baya da kuma laifuka daban-daban domin maido da tsaro a yankunan da ake fama da rikici,” a cewar sanarwar rundunar sojin.

Wannan nasara tana zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da rundunar sojin ta ce ta kawar da wani ɗan ta’adda ɗaya da ƙwato makamai a wani yanki da ’yan Boko Haram suka yi sansani a ƙaramar hukumar Gwoza da ke Jihar Borno.

Sai kuma kisan wasu ’yan ta’addan biyu da ta yi a Garin Rinji da ke Ƙaramar Hukumar Batsari a Jihar Katsina bayan musayar wuta da suka yi, inda ta lalata maɓoyar ’yan ta’addam da kuma ƙwato makamai da wasu kayayyakin.

Jihar Zamfara, inda a can aka kashe Junaidu Fasagora, ta yi ƙaurin suna a wajen tashe-tashen hankula da hare-haren da ’yan bindiga ke yawan kai wa al’ummominta inda suke sace mutane da kashe su.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana