An kashe ƴan fashin daji 22 a Katsina

Rundunar sojin  sama ta ƙasa ta  kashe ƴan fashin daji 22 yaran marigayi Abdulkareem Boss a jihar Katsina. Dakaraun Operation Hadarin Daji ne suka kai hare-haren a Batsari da Sola Poli II dake ƙananan hukumomin Batsari da Jibia. Majiyar Aminiya ta ce ƴan fashin da aka harbe su ne ke kai hare-hare tare da garkuwa […]

An kashe ƴan fashin daji 22 a Katsina

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Rundunar sojin  sama ta ƙasa ta  kashe ƴan fashin daji 22 yaran marigayi Abdulkareem Boss a jihar Katsina.

Dakaraun Operation Hadarin Daji ne suka kai hare-haren a Batsari da Sola Poli II dake ƙananan hukumomin Batsari da Jibia.

Majiyar Aminiya ta ce ƴan fashin da aka harbe su ne ke kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

’Yan fashin daji sun kashe ’yan uwan juna biyu a Kaduna

An kwato shanu kusan 800 daga ’yan fashin daji a Kaduna

A ranar Agusta 6, 2022 ne rundunar sojin sama ta ƙasa ta hallaka Abdulkareem Boss da wasu daga cikin yaransa a Dajin Rugu dake jihar Katsina.

Marigayi Abdulkareem Boss ne ake zargi da kisan kwamanda shiyyar Dutsin-ma na rundunar ƴan sanda a ranar Yuli 5, 2022.

Kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da kashe ƴan fashin dajin sai dai bai bada bayanin farmakin ba.

’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo

Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad

Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC