An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

Da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan bangar tare da yin garkuwa da ’yan matan.

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan.

Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari.

Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da aka sace zuwa dajin Kwangel.

Ɗaya daga cikin majiyar ta ce, ’yan bindigar sun shiga gida gida a lokacin da suka kai farmakin cikin dare.

“Harin da aka kai a daren Laraba shi ne na uku a cikin mako guda. Tun bayan sasantawa da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi da su, sun yi ta kai mana hari. Tattaunawa da sasantawa da mazauna Birnin Gwari ba su amfanar da mu ba.

“Waɗannan hare-haren sun sake dawowa tun ranar da Jihar Kaduna ta sasanta da su a Birnin Gwari. A makon da ya gabata, sun zo sun yi garkuwa da mutane ciki har da mai unguwar. Sun zo sau biyu kafin daren Larabar,” in ji shi.

Shugaban Ƙaramar hukumar Rafi, Ayuba Usman Katako ya tabbatar da faruwar harin a cikin wani shirin Hausa mai suna Tsalle Ɗaya ta gidan rediyon Prestige FM, inda ya ce akwai buƙatar gwamnatocin Neja da Kaduna su haɗa kai don ganin an samu zaman lafiya a jihohin biyu.

“Gaskiya ne ’yan bindiga sun kai hari a unguwar Pandogari. Hasali ma, ba wannan ne kawai harin da aka kai a makonni biyun da suka gabata ba. Harin na Laraba shi ne na uku.