An kashe almajiri an kwakule idonsa a Jigawa

Wasu da ba san ko su wane ne ba sun kashe wani almajiri sannan suka kwakule idonsa a Jihar Jigawa.

An kashe almajiri an kwakule idonsa a Jigawa

Wasu da ba san ko su wane ne ba sun kashe wani almajiri sannan suka kwakule idonsa a Jihar Jigawa.

An tsinci gawar ce bayan an jima ana neman shi, kafin daga bisa aka tsinci gawarsa kwance cikin jini an kwakule masa ido daya.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce kafin a gano gawar, malamin almajirin ya kai rahoto caji ofis cewa tun da yaron ya je neman ice ba a sake jin duriyarsa ba.

Kakakin rundunar, Lawal Shiisu, ya ce malamin mai suna Malam Muhammad Mustafa, “ya yi mana korafi tun da misalin karfe 8 na safiyar Juma’a wani almajirinsa ya tafi nemo ice amma bai dawo gida ba.

“Daga baya aka tsinci gawar almajirin an kwakule masa ido daya,” a kai ta Babban Asibitin Dutse inda likita ya tabbatar ya rasu.

A cewar Shiisu, rundunar ’yan sandan ta fara farautar wadanda suka yi wannan aika-aika.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara