An kashe amarya kwana 10 bayan bikinta
An iske gawar wata amarya mai kimanin shekara 20, mai suna Zainab Yusuf a gidan mijinta da ke Sabuwar Gandu da ke karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.Aminiya ta samu labarin cewa an kashe amaryar ce bayan kwana 10 da yi mata aure a ranar 2 ga Yunin nan. Kuma ana zargin makasanta sun yi […]

An iske gawar wata amarya mai kimanin shekara 20, mai suna Zainab Yusuf a gidan mijinta da ke Sabuwar Gandu da ke karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Aminiya ta samu labarin cewa an kashe amaryar ce bayan kwana 10 da yi mata aure a ranar 2 ga Yunin nan. Kuma ana zargin makasanta sun yi amfani ne da kuranga suka tsallaka katangar gidan.
Angon marigayiyar Malam Inuwa Idris wanda daraktan watsa labarai ne a Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Kano ya shaida wa Aminiya yadda ya samu gawar amaryar tasa “Bayan na tashi daga aiki misalin karfe biyar da rabi na yamma sai na nufi gidana da ke Sabuwar Gandu. Kamar yadda na saba idan na isa gidan zan yi hon ta zo ta bude kofa, amma sai na ji shiru, lamarin da ya sa na kara yin wani hon na biyu. Da na ga babu alamunta sai na fito daga motar na kwankwasa amma shiru, don haka sai na yi anfani da mabudin da ke wurina na bude kofar gidan na shiga. A nan ma ban ji motsinta ba, sai na ci gaba da kiran sunanta. Sai na kewaya ta wata ’yar hanya da za ta kai mutum ga falonmu a nan ne na ga tsani a ajiye, da na daga kaina kuma sai na ga wayar da ta kewaye gidan babu ita babu dalilinta. Nan da nan na yi saurin shiga falonmu a nan na iske marigayiyar kwance kamar tana barci. Amma da na yi magana sai na ji babu wani alamu na rai. Sai kuma na kula jini ya dan fito daga hancinta da bakinta. A gefe guda kuma ga wukar kicin dinsu da kuma filaya.” inji shi.
Aminiya ta samu labarin makasan Zainab sun yi awon gaba da akwatuna biyu babba da karami na kayan lefenta da kuma wasu suturunsu dinkakku ita da maigidan da kuma takalmin maigidan kafa daya.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce bayan mijin marigayiyar ya sanar da hukumarsu sun kai samame unguwar inda suka kama wasu mutane, kuma a yanzu haka sun fara bincike a kan lamarin.
Idan dai za a iya tunawa wannan shi ne karo na biyu da ake samun gawar amaren da ba su dade da aure ba a unguwar ta Sabuwar Gandu a ’yan watannin nan.