An kashe babban dan sanda a arangama da sojoji a Legas
An kashe wani hafsan dan sanda mai mukamin ASP a wata arangama tsakanin ’yan sanda da sojojin ruwa a Jihar Legas.
Sojoji sun kashe wani hafsan dan sanda mai mukamin ASP a wata arangama tsakanin ’yan sanda da sojojin ruwa a Jihar Legas.
Dan sandan mai suna ASP Abion Hezikel ya gamu da ajalinsa ne bayan an caka masa wuka, a yayin da wasu mutum uku suka samu munanan raunuka a rikicin da aka yi a karshen mako.
Wani dan sanda da ya nemi a boye sunansa saboda ba shi da izini iya ce: “Sojojin ruwan sun caka wa jami’anmu wutar soji, muka kai su tare da wasu mutum uku zuwa wani asibiti mai zaman kansa.
“Amma ASP Abion Hezikel ya rasu, kamar yadda likita ya shaida mana. Sauran jami’an namu da mutum ukun kuma suna samun kulawa a sibiti.”
Wasu majiyoyi sun ce sojojin ruwan sun casa masu wucewa da suka nemi sasanta rikicin da ya barke a tsakanin nasu da ’yan.
Wani direban motar haya, Steven Ogbodeto, ya ce ya hangi sojojin da ’yan sanda suna gardama kan wani abu da bai sani ba; Ya ce bayan ya tsaya ana kokarin sasanta su, sai sojojin suka tayar da rikici suka fara fada da ’yan sandan.
Wasu majiyoyi sun ce jami’an sojojin ruwan sun kuma casa masu wucewa da suka nemi sasanta rikicin da ya barke a tsakaninsu.
Da yaek tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin ’yan sanda na Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce suna gudanar da bincike, amma, “An tsare sojoji biyu, wasu biyu kuma sun tsare, amma mun sanar da shugabannin soji domin su mika mana sauran jami’an nasu da suka tsere.”
Ya ce an tura lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifukan Rundunar (SCIID), Panti, Yaba, sannan an kai gawar mamacin dakin ajiyar gawa da ke Yaba.
Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa da ke Yankin Yamma, Edward Yeibo, ya ce rikicin ya barke tsakanin wasu kananan jami’an sojin ruwan da ’yan sanda ne kan cinkoson ababen hawa.
Yeibo, ya ce ana cikin haka ne ’yan sanda da wasu zauna-gari-banza da suka isa wurin suka fara fada da sojojin.
Ya ce, “Wasu ’yan sanda na zuwa wurin a kan babura suka fara harbi, amma yanzu muna gudanar da bincike domin gano hakikakin abin da ya faru, idan mun kammala za mu sanar da jama’a.”