An kashe Bafulatani da dansa kuma an sace ’ya’yansa mata
Wasu mahara da ake zargin sun fito ne daga dajin Kweri a iyakar Abuja da Kaduna, sun kashe wani Bafulatani mai suna Alhaji Buba Bollowa da dansa a gidansa da ke kusa da Bwari a Birnin Tarayya, Abuja. ’Yan uwan marigayin sun shaida wa Aminiya cewa maharan wadanda suka kai 13 sun auka gidan marigayin […]
Wasu mahara da ake zargin sun fito ne daga dajin Kweri a iyakar Abuja da Kaduna, sun kashe wani Bafulatani mai suna Alhaji Buba Bollowa da dansa a gidansa da ke kusa da Bwari a Birnin Tarayya, Abuja.
’Yan uwan marigayin sun shaida wa Aminiya cewa maharan wadanda suka kai 13 sun auka gidan marigayin a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 10:00 na dare dauke da bindiga inda suka jikkata dan uwansa da wani dansa, suka sace ’ya’yansa mata biyu.
Aminiya ta samu labarin cewa maharan sun bar lambar waya da suka ce za a iya samunsu don kai musu fansar kudi kafin su sako ’yan matan.
Wata majiya ta ce a watan jiya ma wasu mahara da ake ji daga dajin suke, sun kai hari a gidan dan uwan marigayin a kusa da Lapai ta Jihar Neja inda suka sace ’ya’yansa biyu, sai da aka biya su Naira miliyan daya da rabi kafin su sako su. Majiyar ta ce kuma wata shida baya an kashe wasu ’yan kasar waje biyu da suka ratsa yankin a kan manyan babura (power bike) za su je Kaduna.
Kakakin ’Yan sandan Abuja ASP Anjuguri Mamzah ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun kama dan uwan marigayin mai suna Ahmadu Sule a kauyen Gina da ke yankin Kagarko a Jihar Kaduna bisa zarginsa da hannu a lamarin bayan binciken sirri.