An kashe dakaru 100 a kwalejin horas da sojoji a Syria
Babu makawa za mu mayar da martani saboda wannan rashin imani ne.
Wani harin jirgi mara matuki da aka kai kan kwalejin horas da kananan sojoji a Syria ya hallaka sojoji fiye da 100, kuma tuni kafofin yada labaran kasar suka zargi kungiyoyin ta’adda.
Bayanai sun ce harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin yaye kananan sojoji a sansaninsu da ke kan iyakar kasar, wanda ya kashe mutane 100, yayin da ake fargabar adadin ka iya karuwa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Amicewa Da Yarjejeniya A Takarda Zai Iya Jefa Ka A Rigima
- An kori karen Joe Biden daga White House saboda yawan cizon mutane
Wannan na zuwa ne bayan harin da Turkiyya ta kai kan mayakan Kurdawa na PKK da ya kashe mutane 9, abin da ke zama tamkar mayar da martani kan harin da kungiyar ta kai Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Turkiyya a farkon makon da muke ciki.
Har yanzu dai babu wata kungiya ko kuma kasa da ta dauki alhakin kai wannan harin da ya rutsa har da fararen hula.
Kamfanin Dillancin Labaran Syria ya ruwaito cewa kawo yanzu harin ya yi sanadiyyar jikkata mutane kusan 200, dalili ke nan da ya sa ake fargabar adadin mamatan ka iya karuwa.
Tuni kwamandan kwalejin horas da kananan sojojin da harin ya shafa, ya ayyana shi a matsayin rashin imani, yana mai cewa babu makawa za su mayar da martani.