An kashe dan kwallon U-20 a Legas

Rundunar tsaro ta ’yan sanda da ke Legas ta ce ta samu nasarar cafke wani matashi dan kimanin shekara 22 mai suna Adebayo Hammed saboda zarginsa da laifin dabawa wani dan kwallon U-20 Onawo Samuel fasasshiyar kwalba a kirji da kuma wasu sassan jikinsa al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.Rundunar ta ce yanzu haka wanda […]

An kashe dan kwallon U-20 a Legas
An kashe dan kwallon U-20 a Legas

Rundunar tsaro ta ’yan sanda da ke Legas ta ce ta samu nasarar cafke wani matashi dan kimanin shekara 22 mai suna Adebayo Hammed saboda zarginsa da laifin dabawa wani dan kwallon U-20 Onawo Samuel fasasshiyar kwalba a kirji da kuma wasu sassan jikinsa al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Rundunar ta ce yanzu haka wanda ake zargin ana tsare da shi a gidan yari a Jihar Legas inda ake cigaba da gudanar da bincike.
Rahoton ya nuna Samuel ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake jiran mota (bas) a tashar mota ta Oyenekan da ke yankin Agege na Jihar Legas. An ce wadansu gungun matasa ne suka yi masa kawanya inda suka bukaci ya  ba su kudi shi kuma ya kekasa kasa ya ce ba zai ba su ko sisin kwabo ba al’amarin da ya fusata shugabansu Adebayo Hammed inda ya caka masa fasasshiyar kwalba a kirji da kuma wadansu sassan jikinsa.  Nan take marigayin ya fadi kasa matacce yayin da suka ranta cikin na-kare.  
Sai dai bayan jami’an ’yan sanda sun tsananta bincike ne suka samu nasarar damke Adebayo Hammed inda suka iza keyarsa kotu don a yi masa hukunci.
Rahoton bai bayyana ko an samu nasarar kamo sauran abokan tafiyar Hammed ba ko a’a.
Rahoton ya nuna marigayi Onawo Samuel yana daga cikin wadanda aka gayyata don yi wa kungiyar kwallon kafa ta matasa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) wasa kafin wannan mummunan al’amari ya faru.
Alkalin kotun da ta yanke wa Adebayo hukunci kuma ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yarin Ikoyi na Jihar Legas ta ce za ta cigaba da sauraron karar ce a ranar 23 ga Afrilun, 2016.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa