An kashe dan Mai shari’a Uwais da ya shiga ISIS a Syria
Ibrahim Uwais, dan tsohon Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Mohammed Lawal Uwais da aka ce ya shiga kungiyar ISIS ya rasu. Wata majiyar iyalansa ta ce an kashe Ibrahim Uwais ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da wani jirgin yakin Amurka ya kai hari ga wani sansanin mayakan ISIS a kusa da garin […]
Ibrahim Uwais, dan tsohon Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Mohammed Lawal Uwais da aka ce ya shiga kungiyar ISIS ya rasu. Wata majiyar iyalansa ta ce an kashe Ibrahim Uwais ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da wani jirgin yakin Amurka ya kai hari ga wani sansanin mayakan ISIS a kusa da garin Aleppo da ke kasar Syria.
Yayar Ibrahim, mai suna Maryam Uwais ne ta bayyana labarin rasuwarsa a shafinta na Facebook, inda ta bayyana shi da mutum mai gaskiya.
“Cike da bakin ciki da kaduwa a zuciyata, na rasa dan uwana Ibrahim Uwais wanda ya rasu a jiya. Dukanmu muna sonsa. Wadanda suka san shi, don Allah ku yafe masa kuma ku yi masa addu’ar Allah Ya gafarta masa dukkan zunubansa,” inji ta.
Ta kara da cewa: “Shi mutum ne da ya fita daban; mai gaskiya da bai karya. Mutum mai yin komai kai-tsaye mai cika alkawari. Ina son Ibrahim kuma ina yi masa addu’a Allah Ya hada mu a Aljannar Firdausi.”
Wata majiya ta kusa da iyalan ma ta tabbatar da rasuwar Ibrahim a Syria, sai dai ba Maryam ce ta bayyana inda dan uwanta ya rasu ba.
Ibrahim mai shekara 41, ya fice ne a asirce tare da matansa biyu da ’ya’yansa biyar zuwa Syria a watan Fabrairun bara don hadewa da kungiyar ISIS.
Lokacin da Mai shari’a Uwais ya samu labarin bacewar dansa da iyalinsa ya shiga damuwa inda ya kaddamar da bincike, daga baya aka gano Ibrahim ya tafi Syria ne ta bi ta kasar Turkiyya.