An kashe daruruwan masu zanga-zanga a Iran  – Amnesty International

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta ce zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 304 cikinsu har da yara 12. Ta ce hukumomin Iran na ci gaba da nuna “mummunar danniya,”  kan masu yin zanga-zangar. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a […]

An kashe daruruwan masu zanga-zanga a Iran  – Amnesty International

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta ce zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 304 cikinsu har da yara 12. Ta ce hukumomin Iran na ci gaba da nuna “mummunar danniya,”  kan masu yin zanga-zangar.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, kungiyar mai kare hakkin dan Adam wacce ke da hedkwata a birnin Landan, ta ce hukumomin kasar suna “Kame irin na mugunta,” inda suke kama dubban masu zanga-zanga da ’yan jarida da ’yan rajin kare hakkin bil Adama da dalibai da ‘nufin hana su kalubalantar mulkin kama-karya,’ da mahukuntan kasar Iran ke  yi.

A cikin wata sanarwa Daraktan Kungiyar Bincike da Tsaro na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, Philip Luther ya ce:

“Gwamnatin Iran ta fara matsin lamba don jefa tsoro da nufin hana shaidu yin magana, saboda tsoron cewa an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar a duk fadin kasar. Maimakon ci gaba da wannan mummunan yakin zalunci, hukumomin Iran ya kamata  su hanzarta sakin wadanda suka tsare ba tare da sharadi ba.

“Jami’an tsaron Iran sun bude wuta kan masu zanga-zanga marasa makami wadanda kuma ba sa haifar da hadari, kuma sun harbi mutane da bindigogi a kai da zuciya da wuya da sauran gabobin muhimmai da niyyar kashe mutane,” inji Amnesty.

Sanarwar ta kuma nuna cewa, an tsare dubban mutane, tare da azabtar da dimbin mutanen da suka hada da yara ’yan kasa da shekara 15 da kuma wadanda ake tsare da su a barikin sojoji ko makarantu.

A tsakiyar watan jiya ne zanga-zanga ta barke, bayan da gwamnati ta yi shelar karin farashin man fetur a daidai lokacin da ake fama da radadin takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar.