An kashe DPO da wasu jami’ansa a Fatakwal

Wasu ’yan bindiga sun kashe DPO mai kula da ofishin  Rumuokoro a karamar Hukumar  Obio/Akpor, Jihar Ribas, Cliff Igwegbe da kuma abokin aikinsa, wani ma mukamin Babban Sufurtanda (CSP).’Yan bindigar sun kuma kara kashe wani babban jami’in ’yan sanda mai kula da sashin aikata miyagun laifuffuka a gundumar Igwuruta, shi ma wadanda ba a san […]

An kashe DPO da wasu jami’ansa a Fatakwal
An kashe DPO da wasu jami’ansa a Fatakwal

Wasu ’yan bindiga sun kashe DPO mai kula da ofishin  Rumuokoro a karamar Hukumar  Obio/Akpor, Jihar Ribas, Cliff Igwegbe da kuma abokin aikinsa, wani ma mukamin Babban Sufurtanda (CSP).
’Yan bindigar sun kuma kara kashe wani babban jami’in ’yan sanda mai kula da sashin aikata miyagun laifuffuka a gundumar Igwuruta, shi ma wadanda ba a san ko su wane ne ba ne suka yi masa kwanton bauna a yankin Elele a karamar Hukumar Ikwerre. An ruwaito cewa akwai karin wani jami’in da wasu da ake zato ’yan kungiyar asiri ne suka daba wa wuka a unguwar Waterfront.
Ahmad Muhammad, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas ya tabbatar wa manema labarai da aukuwar hakan.