An kashe fararen hula 1,153 da soja 105 a wata 3 a Najeriya

An kashe mutum 495 a Zamfara da jami’an tsaro 176 a sassan Najeriya.

An kashe fararen hula 1,153 da soja 105 a wata 3 a Najeriya

An kashe fararen hula akalla 1,153 da jami’an tsaro 176 a Najeriya a cikin wata ukun da suka gabata, watan Yuli zuwa Satumban 2021.

Alkaluman da cibiyar binciken tsaro ta SBM ta fitar sun nuna kashe-kashen sun fi kamari a yankin Arewa maso Yamma inda aka kashe mutum 961, ciki har da mutum 495 da kashe su a Jihar Zamfara.

Jami’an tsaron da aka kashe sun hada da soja 105, ’yan sanda 67, jami’an shige da fice biyu da kuma jami’an kwastam da sibil difens daya-daya a tashe-tashen hankula a sassan Najeriya.

Cibiyar bincken, wadda ta tattaro tare da sharhin abubuwan da ke faruwa a sassan Najeriya, ta hada rahoton nata ne daga rahotannin kafafen yada labarai kan kashe-kashen kungiyar Boko Haram, ’yan binidiga, kungiyar IPOB, ’yan kungiyar asiri da sauran bata-gari.

Kididigar, wadda ba ta fayyace adadin mutanen da ’yan bindiga ko kungiyar Boko Haram suka hallaka ba, ta ce kungiyar IPOB ta kashe mutum 29, ’yan kungiyar asiri sun kashe mutum 27, ’yan fashi kuma sun kashe mutum 24.

Masu garkuwa da mutane kuma sun kashe 23 sai ’yan banga da suka hallaka mutum 10.

Rahoton ya nuna an kashe mutum 961 a yankin Arewa maso Yamma ya kara da cewa an kashe mutum 646 a Arewa ta Tsakiya.

Yankin Arewa maso Gabas shi ne a matsyi na uku da adadin mutm 336 da aka kashe a cikin wata ukun.

Yankin Kudu maso Gabas shi ne a matsayi na hudu, inda aka kashe mutum 137; sai Kudu masu Kudu, mutum 105; sannan Kudu maso Yamma, mutum 102.

Rahoton ya kuma nuna kashe-kashen da aka yi a Jihar Imo su ne mafiya muni a daukacin yankin Kudu, inda aka kashe mutum 59.

Da yake jawabi, Shugaban Darikar Katolika a yankin Arewa, Rabaran Mathrew Kukah, ya ce yawan kashe-kashen da ke faruwa alama ce ta yawan aikata sabon Allah a Najeriya.

Bishop Kukah ya bayyana haka ne a taron cika shekara 120 na cocin Afirka, da addu’ar hadin kai.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su rika bayar da kwarin gwiwa da kuma kulawa ga mutanen da matsalar rashin tsaro ta shafa.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya