An kashe fararen hula 5 a birnin Timbuktu
Akwai sama da mutum 20 da suka jikkata a harin.
Bayanan da ke fitowa daga birnin Timbuktun Arewacin kasar Mali, na tabbatar da salwantar rayukan akalla fararen hula biyar a wani hari na baya-bayan nan da aka kai kan al’umma.
Sabon harin da cikakkun bayanansa ke fitowa a wannan Asabar bayan kai shi a ranar Alhamis, ya zo ne wata guda da rabi bayan kawanyar da mayakan tarzoma suka yi wa Timbuktun.
- Gidauniyar Noma ta nemi gwamnati ta keɓe Ranar Manoma
- Matsalar rashin zuwan mata makaranta ta fi tsanani a Arewacin Najeriya — UNICEF
Tabbacin harin ya fito cikin wata hirar da gwamnan yankin Bakoun Kante ya yi da kafofin watsa labaran cikin kasar, kuma ya ce tuni aka yi jana’izar wadanda suka mutun.
Wasu cibiyoyin lafiya ma dai sun ruwaito cewa akwai sama da mutum 20 da suka jikkata a harin.
Daga cikin wadanda suka salwantan kuma har da wasu kananan yara, kamar yadda shaidu suka tabbatar.