An kashe fararen hula 8 a Arewacin Mali

Wani ɗan majalisar yankin,ya ce cikin waɗanda suka mutu har da wani jami’in lafiya mai kula da shirin rigakafi a Intadeyni.

An kashe fararen hula 8 a Arewacin Mali

Aƙalla fararen hula takwas ne suka mutu sakamakon wani hari ta sama da aka kai kan wata mota a kusa da iyakar Mali da Nijar, kamar yadda majiyoyin yankin da na tsaro suka bayyana.

Majiyoyin sun ce mutanen na kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a garin Inkadewane, mai nisan kusan kilomita 50 daga birnin Menaka, lokacin da aka kai harin ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa zuwa yanzu babu wata ƙungiya ko hukuma da ta ɗauki alhakin kai harin.

Wata majiya daga yankin ta ce dukkan fasinjojin da ke cikin motar, ciki har da matasa ƙanana, sun mutu nan take.

Wani ɗan majalisar yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce cikin waɗanda suka mutu har da wani jami’in lafiya mai kula da shirin rigakafi a cibiyar lafiya ta Intadeyni.

Ya bayyana lamarin a matsayin babban abin takaici, yana mai cewa yankin Menaka na da matuƙar buƙatar ma’aikatan lafiya.

A cikin ’yan makonnin nan dai, sojojin Mali da dakarun Africa Corps masu goyon bayan Rasha sun ƙara kai hare-hare bayan manyan hare-haren da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda da ƙawayenta ’yan tawayen Tuareg suka kai a ƙarshen watan Afrilu, inda har Ministan Tsaron Mali ya rasa ransa.

Gwamnatin mulkin soja ta Mali ta ƙara tsaurara matakan tsaro, ciki har da haramta amfani da babura masu ƙarfin injin da ya haura 125cc a wajen manyan birane, saboda mayaƙan masu iƙirarin jihadi na amfani da su wajen kai hare-hare.

Wata majiya ta tsaro ta ce tafiya da motocin ɗaukar kaya da babura a yankunan ta zama babban haɗari ga fararen hula, musamman tun bayan hare-haren da aka kai a ƙarshen watan Afrilu.

A ranar Litinin kuma, ƙungiyar Africa Corps ta wallafa wani bidiyo da ta ce ya nuna yadda ta lalata wata mota da jirgi marar matuƙi, tana zargin motocin na ɗauke da makamai ne na mayaƙan da take kira ’yan ta’adda.

A wannan rana, ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi mayaƙan JNIM, ’yan tawayen Tuareg, sojojin Mali da kuma dakarun Africa Corps da aikata munanan laifuka na take haƙƙin fararen hula bayan hare-haren da suka faru a watan Afrilu.