An kashe mutanenmu 350 a Filato —Kungiyoyin Fulani

Ƙungiyoyin Fulani sun yi ikirarin an kashe mambobinsu 350 baya ba asarar shanu 834 a watanni uku da suka gabata a Jihar Filato

An kashe mutanenmu 350 a Filato —Kungiyoyin Fulani

Gamayyar kungiyoyin Fulani sun yi ikirarin an kashe mambobinsu 350 baya ba asarar shanu 834 a watanni uku da suka gabata a Jihar Filato.

Kungiyoyin Fulanin sun ce an yi wa Fulani wannan aika-aika ne tsakanin Oktoban  2023 da Janairu 2024 a kananan hukumomin Barikin Ladi, Bokkos da Mangu na jihar.

Karon farko ke nan da shugabannin al’ummar Fulani suka fito suka  yi magana kan da hare-haren da kai a kananan hukumomin, inda aka kashe sama da mutane 190.

A wani taron manema labarai karkashin jagorancin shugaban kungiyar MACBAN na jihar a Jos, Malam Nura Adullahi, kungiyoyin sun ce Fulani sun fuskanci cin zarafi da tsoratarwa baya ga kisan gilla da ake musu a sassan jihar.

A cewar MACBAN “daga ranar 29 ga Agusta zuwa 24 ga Disambar 2023, an sace shanu 834 a kananan hukumomin Bokkos da Mangu.

“A farko-farkon bara ne ’yan fashin suka fara kai wa Fulani munanan hare-hare a karamar hukumar Mangu a tsakanin 14 ga watan Afrilu zuwa 15 ga watan Yuli, inda aka yi wa Fulanin sama da 350 kisan gilla aka kona kauyuka sama da 115 kurmus, aka lalata dukiyoyi da kayan abinci.”

Nura ya kuma ce “jimillan ’yan gudun hijira 23,515 na zaune a sansanoni gudun hijira da gidajen ’yan uwa da ke jihohin Bauchi, Kaduna, Nasarawa da Taraba.”

“An kuma yi asarar dukiyoyi na biliyoyin nairori a wannan ta’asa, wadda ta sa Fulani kaura daga wasu gundumomi takwas da suka hada da Mangu, Panyam, Pushit, Kerang, Bwoi, Kombun, Ampang da Mangum.”

Al’ummar Fulanin da aka raba sun hada da Bwoi, Kombun, Sarfai, Rinago, Jukga, Kuwes, Kaangag, Farinkasa, Kerana, Lugga, Dimeza, Fungong, Gindirin, Gok, Bunghan, Gida, Milet, Rufwang, Dejwak, Lupo, Wushik da sauransu.

Ya bayyana cewa bayanin duk ta’asar da aka yi musu na cikin rahoton hukumomin tsaro a jihar.

Kungiyoyin sun yi kira ga mambobinsu da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu, sannan suka bukaci hukumomin tsaro da su binciki abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan da kuma tabbatar da adalci.

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu