An kashe fursunoni 129 a garin tserewa daga kurkuku a Congo

Mutane 129 sun mutu a lokacin da fursunoni suka yi kokarin tserewa daga gidan yari mafi girma a kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

An kashe fursunoni 129 a garin tserewa daga kurkuku a Congo

An kashe mutane 129 a yunkurin fursunoni na tserewa daga gidan yari mafi girma a kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Kasar ta ce fursunoni 24 sun mutu ne sakamakon raunin harbi, bayan jami’an tsaro sun yi harbin gargadi a lokacin boren na ranar Litinin.

Sauran kuma sun mutu ne a sakamakon sarkewar nunfashi da turmutsutsin da aka samu a gidan yarin na Makala da ke Kinshasa, babban birnin kasar.

Kimanin shekaru bakwai ke nan da wasu fursunoni 4,o00 suka tsere daga gidan yarin.

A ranar Litinin makwabtan gidan yarin suka ce sun fara jin karar harbe-harbe a ciki, amma ’yan sanda ba su bar manema labarai sun shiga wurin.

Wani mazaunin yankin, Daddi Soso, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Da misalin farfe 01:00 ko 02:00 na dare muke fara jin karar harbe-harbe har zuwa kare 05:00 na asuba.

“An kashe wasu fursunoni kuma wasu sun tsere,” in ji shi, amma ya ce jami’an tsaro sun fara kwashe gawarwakin.

Wani mai suna Mr Shabani ya wallafa a shafinsa na X bayan lamarin cewa, akalla mutane 60 sun samu munanan raunuka kuma an kai su asibiti.

Hukumomin kare hakkin dan Adamun sun bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.

An gina gidan yarin Makala ne a shekarun 1950 da karfin daukar fursunoni 1,500, ammma a halin yanzu sama da fursunoni 14,000 ke tsare a cikinsa.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda