An kashe gobarar da ta tashi a Matatar Dangote

Babu wata damuwa domin matatar man fetur ɗin na ci gaba da tafiyar da lamurranta.

An kashe gobarar da ta tashi a Matatar Dangote

Gobara

Mahukunta Matatar Man Fetur ta Dangote ta ce matatar na ci gaba da aiki yadda ya kamata bayan wata gobara da ta kama a yau Laraba.

A cikin wata sanarwa da matatar ta wallafa a shafinta na X ta ce, “Mun samu nasarar kashe wata ƴar gobara da ta tashi a kamfaninmu yau Laraba 26 ga watan Yuni.

Sanarawar mai dauke da sa hannu mai magana da yawun matatar Anthony Chiejina ta ce, “Babu wata damuwa domin matatar man fetur ɗin na ci gaba da tafiyar da lamurranta sannan kuma babu wanda ya samu rauni.”

Aminiya ta ruwaito cewa, an samu tashin gobara a wani sashe na matatar Dangote da ke Ibeju Lekki a Legas da safiyar Laraba.

Sai a lokacin ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba, amma an bai wa ma’aikatan matatar umarnin gaggauta ficewa daga cikinta.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano