An kashe jagoran ’yan bijilanti a Kano

Tuni an cafke ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannun a lamarin.

An kashe jagoran ’yan bijilanti a Kano

Taswirar Kano

Ana fargabar kashe wani jagoran ’yan bijilanti a Unguwar Ja’en da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, Mukhtar Garba Baballiya.

Bayanai sun ce an soka wa Baballiya wuƙa ne a daren ranar Talata yayin da yake ƙoƙari sulhunta rikicin da ya ɓarke tsakanin wasu ɓata-gari a Ja’en Makera da Ja’en Unguwar Lalle.

An dai yi gaggawar miƙa Baballiya Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed inda nan likitoci suka tabbatar da ya ce ga garinku nan.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni an cafke ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannun a lamarin.

Kiyawa ya buƙaci mazauna da su gaggauta miƙa wa ’yan sanda rahoton duk wani lamari da ke barazana ga zaman lafiya yayin da bayar da tabbacin za su ci gaba da bincike.

A bayan nan an samu rahoton faɗan daba a wasu yankunan Birnin Dabo musamman Unguwar Dorayi da Dala.

Aminiya ta ruwaito yadda wani rikici ma faɗan daba ya yi ajalin mutane uku a Unguwar Darmanawa da ke jihar

Shin Binani ta dawo?

Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi