An kashe jami’an tsaro biyu a arewa maso gabashin Iran

Jami’an tsaron sun rasa rayukansu ne yayin da suke sintiri a birnin Mashhad, kimanin kilomita 15 daga hubbaren Imam Reza.

An kashe jami’an tsaro biyu a arewa maso gabashin Iran

US army soldiers stand near armoured military vehicles on the outskirts of Rumaylan in Syria’s northeastern Hasakeh province, bordering Turkey, on March 27, 2023. (Photo by Delil souleiman / AFP) (Photo by DELIL SOULEIMAN/AFP via Getty Images)

Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe jami’an tsaro biyu a wani hari da aka kai a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce waɗanda aka kashe mambobi ne na rundunar Basij, wata rundunar sa-kai da ke ƙarƙashin dakarun rundunar juyin juya hali ta IRGC.

Sai dai rahoton bai bayyana ranar da harin ya faru ko kuma waɗanda suka kai harin ba, amma ya ce za a hukunta waɗanda suka aikata lamarin.

A cewar Tasnim, jami’an tsaron sun rasa rayukansu ne yayin da suke sintiri a birnin Mashhad, kimanin kilomita 15 daga hubbaren Imam Reza, wurin ibada mafi tsarki ga mabiya Shi’a a Iran, inda aka binne marigayi Jagoran Addinin ƙasar, Ali Khamenei, da safiyar Juma’a.

Lamarin na zuwa ne yayin da rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka a wannan mako, inda ɓangarorin biyu suka yi musayar hare-hare mafi muni tun bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan da ya gabata, wadda ta tabbatar da tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilu.

Tags