An kashe Janar din Sojin Rasha a harin bam a Moscow

Rasha na zargin abokiyar hammayarta Ukraine da harin, wanda ya yi ajalisar Laftanar-Janar Fanil Sarvarov.

An kashe Janar din Sojin Rasha a harin bam a Moscow

Inda motar Janar Fanil ta tarwatse a sakamakon harin bom da aka dasa a karkashin motarsa a safiyar Litinin

Wani bom da aka dasa a karkashi mota ya kashe wani Janar din sojan Rasha a birnin Moscow a ranar Litinin.

Laftanar-Janar Fanil Sarvarov, wanda aka kashe a safiyar Litinin, shi ne Shugaban Sashen Bayar da Horo da Ayyuka na Rundunar Sojin Rasha.

Hukumomin Rasha sun ce Janar Sarvarov ya rasu ne sakamakon munanan raunuka a sanadiyyar fashewar bom din da aka dasa a karkashin motarsa.

Masu bincike sun bayyana cewa bom din ya fashe ne bayan motar ta fara tafiya, kuma karafan da suka fito da bom din sun lalata wasu motoci bakwai da ke wurin ajiye motoci da abin ya faru.

Tuni Rasha ta kaddamar da bincike kan musabbabin lamarin, inda take zargin abubuwa da yawa, ciki har da yiwuwar hannun abokiyar yakinta, kasar Ukraine a cikin harin.

Rahotanni sun nuna cewa Janar Sarvarov mai shekara 56, a bayan ya taba aiki a Chechnya, kuma ya gudanar da ayyuka da dama a lokacin hare-haren da Rasha ta kai a yayin rikicin kasar Syria.

A watan Disambar bara, 2024, wani harin bom da aka makala a cikin wani kek mai amfani da wutar lantakri ya kashe Shugaban undunar Kare Sojojin Rasha daga Makaman Nukiliya, Sinadarai da Halittu, Igor Kirilov tare da direbansa a birnin Moscow. Rasha ta zargi hukumar leken asirin Ukraine da hannu a harin.

 

Ukraine ta ki cewa uffan

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa kai tsaye daga Ukraine game da kisan janar ɗin Rasha. A tarihi, Ukrain kan yi shiru kan irin waɗannan abubuwa.

ko da yake an taɓa samun kashe-kashe irin wannan a cikin Rasha. Haka kuma, irin waɗannan hare-hare sun taɓa faruwa a nan Kyiv.

A lokacin bazara, an harbe wani Kanar na rundunar sojin Ukraine har lahira a birnin Kyiv, don haka akwai wannan musayar hare-hare.

Ga Ukraine, wannan wani abu ne da a tarihi suka yi nasara a kai idan aka duba ayyuka kamar Operation Spiderweb, inda ta dasa jirage marasa matuka da yawa a hanyoyin motoci, wanda ya lalata jiragen Rasha da dama a filayen jirgin sama.

‘Ba mu yi tsammani ba’

Mazauna kudancin Moscow, inda bam din ya kashe shugaban Sashen Horon Ayyuka na Babban Hafsin Sojojin Rasha sun bayyana cewa, ba su taba tsammanin haka ba.

“Ba mu taɓa tsammani ba. Mun yi tunanin muna cikin aminci, sai kuma wannan ya faru a kusa da mu,” in ji Tatiana, mai shekaru 74, ga kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Tagogi sun yi girgiza. Za ka iya gane cewa fashewar wani abu ne,” in ji Grigory, mai shekaru 70, wanda ya ƙi bayyana sunansa gaba ɗaya, ga AFP. “Ya kamata mu ɗauki lamarin da natsuwa. Wannan shi ne farashin yaƙi.”

AFP ta ce ’yan jaridanta da ke wurin sun ga wata motar Kia SUV mai launin fari da ta lalace ƙwarai, ƙofofinta da taga na baya sun tarwatse. Jikin motar ya karkace kuma ya ƙone sakamakon fashewar.

An kewaye yankin da jami’an tsaro, kuma masu bincike suna tantance tarkacen da ya rage.

 

Muhimmancin kisan Janar Sarvorov ga Ukraine

Marina Miron, ƙwararriyar mai nazarin harkokin soja da ke Sashen Nazarin Tsaro a King’s College London ta ce hukumomin tsaron Ukraine za su iya sha’awar kashe Sarvarov saboda rawar da yake takawa a dabarun soja, wanda ba za a samu sauƙin maye gurbinsa ba.

“Mai yiwuwa Hukumar Tsaron Ukraine (FDU), za ta iya gudanar da irin wannan aiki, kuma tabbas za su sha’awar kawar da manyan jami’an soja a Rasha, domin janar ɗin yana da matuƙar muhimmanci wajen horar da ayyukan soja,” in ji Miron ga Al Jazeera.

Sarvarov ya kawo wa rundunar sojin Rasha ƙwarewa mai matuƙar muhimmanci a fagen yaƙi da shirye-shiryen dabarun soja, ciki har da a Chechnya, Syria da Ukraine.

“Don haka, yana da muhimmanci ƙwarai a cikin Ma’aikatar Tsaron Rasha – akwai dalilin da ya sa hukumomin tsaron Ukraine za su yi ƙoƙarin kai hari da kawar da irin waɗannan manyan jami’an domin raunana rundunar sojin Rasha a matakin dabarun tsaro,” in ji ta, ta ƙara da cewa maye gurbin irin wannan babban jami’i ba abu ne mai sauƙi ba .

Manyan sojojin Rasha da aka kashe 

Kisan Sarvarov shi ne na baya-bayan nan a jerin kashe-kashen jami’an soja da sauran masu goyon bayan yaƙi tun bayan da Rasha ta kaddamar da cikakken mamayarta a Ukraine a watan Fabrairu 2022.

Ga wasu shahararru daga cikinsu:

1- Laftanar-Janar Yaroslav Moskalik:

Mai shekaru 59, ya mutu sakamakon bam da aka dasa a mota a kusa da Moscow a ranar 25 ga watan Afrilu, 2025. Moskalik shi ne mataimakin shugaban Sashen Babban Ayyuka na Rundunar Sojojin Rasha.

2- Laftanar-Janar Igor Kirillov:

Shugaban Rundunar Kare Sojojin Rasha daga Makaman Nukiliya, Sinadarai da Halittu na Rasha, ya mutu tare da direbansa bayan tashin wani bam da aka ɓoye a keke mai amfani da lantarkia a birnin Moscow a 17 Disamba, 2024.

3- Kyaftin Valery Trankovsky: 

A ranar 13 ga Nuwamba, 2024, wani bam da aka dasa a ƙarƙashin mota ya kashe wani sojan Rasha a Sevastopol, da ke yankin Crimea da Rasha ta mamaye. Wata majiyar tsaron Ukraine ta  ce Kyaftin Valery Trankovsky, daga rundunar ruwa ta Rasha, shi ne wanda Ukraine take zargi aikata laifukan yaƙi saboda umartar harin makamai masu linzami kan fararen hula.

4- Stanislav Rzhitsky:

An harbe Jami’in sojan Rasha da ya jagoranci jirgin ruwan karkashin teku a Bahar Maliya kuma aka saka sunansa a jerin masu laifin yaƙi na Ukraine, Stanislav Rzhitsky, har lahira a yayin da yake gudu domin motsa jiki da safe a birnin Krasnodar na kudu.

5- Vladlen Tatarsky:

Dan jaridar intanet mai goyon bayan yaƙin Rasha, ya mutu sakamakon harin bam da aka ɓoye cikin wani ƙaramin mutum-mutumi da wata mace ta ba shi a wani gidan shan kofi da ke birnin St Petersburg 2 ga Afrilu, 2023.

6- Darya Dugina:

A  ranar 20 ga Agusta, 2022 ’yar wani shahararren mai ra’ayin kishin ƙasa mai goyon bayan yaƙi, ta mutu sakamakon bam da aka dasa a mota a yankin Moscow.