An kashe jarumi da takobi wajen gwajin fim
Wani jarumin fim a kasar Japan ya hadu da ajalinsa, inda aka soke shi da takobi wajen gwajin wasan fim a daukin daukar fina-finai da ke birnin Tokyo, babban birnin kasar Japan.Jami’an ’yan sand asun fara binciken wannan kisan da aka yi wa jarumin fim din, don su tantance tsaklanin gananci ko hadari.Kafafen yada labarai […]
Wani jarumin fim a kasar Japan ya hadu da ajalinsa, inda aka soke shi da takobi wajen gwajin wasan fim a daukin daukar fina-finai da ke birnin Tokyo, babban birnin kasar Japan.
Jami’an ’yan sand asun fara binciken wannan kisan da aka yi wa jarumin fim din, don su tantance tsaklanin gananci ko hadari.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, jarumai da dama na wasannin gwaji a lokacin da al’amarin ya auku ranar Litinin din da ta gaba, amma babu wanda ya ga yadda wannan lamari ya auku.
Wani dan Japan da ke gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon NHK, ya ruwaito cewa, jarumi Daigo Kashino ya halaka ne bayan da aka soke shi a ciki, sun kuma juyo wajensa ne bayan da aka kakarin mutuwa.
Kashino dan 33, jarumi ne da ke aiki a gidan wasa na wajen birnin Tokyo. An yi hanzarin kai shi asibiti, amma sa’o’i kadan da aukuwar lamari, sai kawai ya mutu, a cewar ’yan sanda.
Jami’an ’yan sanda ba su bayar da siffar takobin ba, ta yadda za a tantance kan ko tana da matakan kariya, wadanda za su hana a yi wa mutum rauni.