An kashe kwamandan ISWAP Abou Aisha a Borno

’Yan ta’adda sun yi asara mai yawa, ciki har da wani babban kwamanda da aka ambato da suna Abou Aisha.

An kashe kwamandan ISWAP Abou Aisha a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP da aka bayyana da suna Abou Aisha, yayin da suka daƙile hare-haren da ake zargin ’yan ta’addan sun kai a Pulka da Mandaragirau a Jihar Borno.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar-Kanar Sani Uba, ya fitar, inda ya ce hare-haren sun faru ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2026.

A cewarsa, bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa ’yan ta’addan sun yi asarar rayuka da dama, ciki har da Abou Aisha, wanda ya samu mummunan rauni a wuyansa.

“Bayanan sirri sun tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun yi asara mai yawa, ciki har da wani babban kwamanda da aka ambato da suna Abou Aisha, wanda ya samu mummunan rauni a wuyansa, tare da asarar makamai da kayan aiki masu yawa,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ’yan ta’addan sun yi yunƙurin mamaye wuraren tsaro a Pulka da Mandaragirau, amma sojoji sun daƙile harin ta hanyar amfani da ƙarfin wuta da dabarun yaƙi.

Uba ya bayyana cewa a daren harin, wani babban rukuni na ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun fito daga dajin Sambisa suka kai hari kan sojojin Sashe na 1 da ke Pulka.

Game da harin Mandaragirau kuwa, ya ce mayaƙan ISWAP sun kai hari ne ta amfani da manyan motoci da babura, amma sojoji sun tura ƙarin runduna wadda ta yi nasarar fatattakar maharan bayan musayar wuta mai tsanani.

Ya ƙara da cewa duk da cewa wasu sojoji da mambobin rundunar haɗin gwiwar farar hula sun samu raunuka, an gaggauta kai su cibiyoyin lafiya mafi kusa domin samun kulawa.

A cewarsa, rundunar sojin sama ta Operation Haɗin Kai tare da jiragen saman Sojojin Ƙasa ne suka taimaka wajen jigilar waɗanda suka ji rauni.