An kashe ma’aikatan agaji uku a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
A kalla mutane 22 ne suka rasa rayukansu ciki har da ma’aikatan kungiyar agaji ta likitoci wato (Medecins Sans Frontieres) a garin Nanga Boguila wanda ke da nisan kilomita 450 arewa da babban birnin kasar, Bangui. Wani tsohon dan Majalisar kasar, Gilles dabier Nguembassa ya ce yawancin mutanen da suka mutu sun rasa rayukansu ne […]
A kalla mutane 22 ne suka rasa rayukansu ciki har da ma’aikatan kungiyar agaji ta likitoci wato (Medecins Sans Frontieres) a garin Nanga Boguila wanda ke da nisan kilomita 450 arewa da babban birnin kasar, Bangui.
Wani tsohon dan Majalisar kasar, Gilles dabier Nguembassa ya ce yawancin mutanen da suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin da aka kai wani hari asibitin kungiyar agajin a dai-dai lokacin da dattawan yankin ke gudanar da wani taro inda 15 daga cikinsu suka rasu. Ya kara da cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da mayakan kungiyar musulmi ta Seleka suka kai hari asibitin don dibar kudade. Amma har zuwa lokacin wannan rawotan jami’an kungiyar ta Seleka ba su mayar da martini ba kan zargin.
kasar dai ta fada rikicin addini wanda ya tilasta wa miliyoyin mutane barin muhallansu. Ko a ranar Lahadin da ta gabata ma, dakarun Tarayyar Afirka da kuma na kasar Faransa sai da suka taimaka wa wasu Musulmai fiye da dubu wajen yin hijira daga babban birnin kasar.
Yawancin ‘yan gudun hijiran na isa kasar Chadi ne. Amma wadanda sukai hijira ranar Lahadin sun nufi garuruwan da ke iyakar kasar daga bangaren arewa ne. Majalisar dinkin Duniya dai ta bayyana hare-haren da wani “kisan kiyashi” kan al’ummar Musulman da ke kasar.
Rikicin siyasa da na addini ya yi kamari a kasar, tun bayan wani yunkurin hanbarar da gwamnatin‘yan tawayen Musulmi da wasu Kritoci suka yi a watan Disamban bara. Daga nan ne kuma kungiyar Kristoci ta Anti-Balaka ta fara kai hari ga Musulmai fararen hula da ke kasar.