An kashe ma’aikatan jinkai 4 da yin garkuwa da 2 a Borno
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin maharan Boko Haram ne sun kashe ma’aikatan jinkai hudu sannan suka yi garkuwa da mutum biyu a wani yankin Arewa na Jihar Borno da safiyar yau Lahadi. Wani jami’in agaji ya bayyanawa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun aikata hakan ne da misalin karfe 10 na safe a hanyar garin […]
Hanyar Maiduguri zuwa Monguno
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin maharan Boko Haram ne sun kashe ma’aikatan jinkai hudu sannan suka yi garkuwa da mutum biyu a wani yankin Arewa na Jihar Borno da safiyar yau Lahadi.
Wani jami’in agaji ya bayyanawa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun aikata hakan ne da misalin karfe 10 na safe a hanyar garin Monguno zuwa Maiduguri babban birnin jihar.
‘Yan bindigar sun bude wa ma’aikatan agajin wuta lokacin da suke tafiya sannan suka yi awon gaba da mata biyu.
A cikin wadanda aka kashe akwai jami’in jinkai na Kungiyar Actions Against Hunger, da wani ma’akacin Solidarity International, sannan wani fasto kamar yadda rahoton ya sanar.