An kashe ma’aikatan Red Cross biyu a Yemen
A shekaranjiya Laraba ne aka kashe wasu ma’aikata biyu wadanda ke aiki da kungiyar ba da Agaji ta kasa-da-kasa wato (Red Cross) a yankin arewacin kasar Yemen, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.Ma’aikatan biyu – wadanda dukansu ’yan kasar Yemen ne na tafiya da wani ayarin motoci daga lardin Saada da ke […]
A shekaranjiya Laraba ne aka kashe wasu ma’aikata biyu wadanda ke aiki da kungiyar ba da Agaji ta kasa-da-kasa wato (Red Cross) a yankin arewacin kasar Yemen, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Ma’aikatan biyu – wadanda dukansu ’yan kasar Yemen ne na tafiya da wani ayarin motoci daga lardin Saada da ke arewacin kasar zuwa binin Sana’a.
kungiyar Red Cross ta kwatanta lamarin a matsayin abin mamaki da ba’a taba ganin irinsa ba. Wanda hakan ya sanya kungiyar dakatar da dukkan ma’aikatanta daga zirga-zirga a fadin kasar.
Kisan ma’aikatan ya zo ‘yan kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishinta a birnin Aden da ke kudancin kasar.
Yakin basasar kasar ya yi kamari ne a watan Maris da ya wuce, bayan da hadakar kasashen Larabawa wadanda kasar Saudiyya ke jagoranta ta dakatar da ’yan kabilar Houthi daga fadada ikonta kuma ta dawo da shugaban kasar karagar mulki bayan ya tsere birnin Riyadh.
Fiye da mutum dubu hudu da 500 ne suka rasa rayukansu a rikicin. Kuma tun kafin fara yakin, kasar tana daya daga cikin wadda ta fi talauci a cikin kasashen Larabawa.