An kashe mahara 32 da jami’an tsaro 3 a Borno

Rundunar JTF mai aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno ta ce ta halaka wadanda ake zargi ’yan Boko Haram ne 32 wadanda suka kai hare-hare kan cibiyoyin tsaro a Bama da Malam Fatori.Kakakin JTF Laftana Kanar Sagir Musa, wanda ya bayyana haka ya ce sojoji biyu da dan sanda daya sun rasu a […]

An kashe mahara 32 da jami’an tsaro 3 a Borno
An kashe mahara 32 da jami’an tsaro 3 a Borno

Rundunar JTF mai aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno ta ce ta halaka wadanda ake zargi ’yan Boko Haram ne 32 wadanda suka kai hare-hare kan cibiyoyin tsaro a Bama da Malam Fatori.
Kakakin JTF Laftana Kanar Sagir Musa, wanda ya bayyana haka ya ce sojoji biyu da dan sanda daya sun rasu a lokacin kai harin.
Ya ce an kai harin ne ga hedkwatar rundunar hadin gwiwa ta kasashe uku da (MNJTF) da ke Malam Fatori da Barikin ’Yan sandan Kwantar da Tarzoma da ke Bama.
Ya ce, sojoji biyu da mahara 15 suka halaka a fafatawar Malam Fatori, yayin da dan sanda daya da mahara 17 suka mutu a Bama.
Rashin wayar sadarwa a yankin sakamakon dokar ta-baci da Shugaban kasa Jonathan ya kafa ta hana samun bayanai daga mutanen garuruwa biyu.
Malam Fatori da ke karamar Hukumar Abadam a Jihar Borno da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar ta yi fama da fafatawa a tsakanin jami’an tsaro da maharan Boko Haram, wanda hakan ya tilasta mazauna garin suka tsallaka zuwa garin Bosso da ke Nijar.
Laftana Kanar Sagir ya ce maharan sun yi amfani da miyagun makamai da bama-bamai wajen kai hare-haren da karfe 6:45 na safe ranar 4 ga Agustan nan.
Ya ce a harin Bama sojoji sun kwato kayayyakin da suka hada da: Toyota Hilud guda 4 da bindiga kirar AK 47 guda 10 da bindiga kirar G3 guda 2 da bama-bamai 10 masu nauyin milimita 40 da harsasai da babura uku da sauransu.
A wani labarin kuma sojoji sun gudanar da binciken gida-gida a garin Potiskum a daidai lokacin da aka kafa dokar hana fita daga gida na awa 24 a garin, domin zakulo makamai daga mahara sakamakon bayanan sirrin da suka samu cewa maharan na shirin kaddamar da hare-hare a garin a lokacin bukukuwan karamar Sallah.
Kakakin JTF a Jihar Yobe Kyaftin Eli Lazarus ya bayyana haka cikin wata sanarwa, inda ya ce daukar matakin ya biyyo bayan rahoton sirri cewa marahan sun shiga garin dauke da nakiyoyin da ake zargin sun sato daga wani kamfanin gine-gine na mutanen kasar China cikin dare.
Kafa dokar hana fita a gari na Potiskum wanda ya samu sararawa na wani lokaci ta zo ne bayan shekara daya da kafa irin ta a garin wanda shi ne mafi girma jihar.
Tun a makon jiya ne rundunar JTF a Borno ta ba da sanarwar cewa maharan na shirin kaddamar da miyagun hare-haren a daidai lokacin da aka kammala azumin watan Ramadan.