An kashe mai goyon bayan kulob din Santos da rodi a Brazil

Wani mai goyon bayan kulob din Santos da ke Brazil dan kimanin shekara 31 ya rasa ransa bayan da wadansu magoya bayan kulob din Sao Paulo suka yi masa dukan kawo wuka ta hanyar amfani da rodi jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kungiyoyin kwallon kafar biyu a karshen makon jiya.Rahotannin sun ce […]

An kashe mai goyon bayan kulob din Santos da rodi a Brazil
An kashe mai goyon bayan kulob din Santos da rodi a Brazil

Wani mai goyon bayan kulob din Santos da ke Brazil dan kimanin shekara 31 ya rasa ransa bayan da wadansu magoya bayan kulob din Sao Paulo suka yi masa dukan kawo wuka ta hanyar amfani da rodi jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kungiyoyin kwallon kafar biyu a karshen makon jiya.
Rahotannin sun ce marigayin ya tsaya a kan hanya yana jiran motar bas din da za ta kai shi gida ne a lokacin da matasan cike da motoci biyu na magoya bayan kulob din Sao Paulo suka dirar masa inda suka rika shirgarsa da rodi al’amarin da ya sa zube a kasa warwas kuma kafin a kai shi asibiti ya ce ga garinku.
Wani rahoto ya tabbatar an kashe fiye da mutum 30 a yamutsin kwallo a kasar Brazil a shekarar bara kadai.
Al’amarin yana ci wa hukumomin Brazil tuwo a kwarya musamman ganin yadda kasar ce za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya da zai gudana a watan Yunin wannan shekara.
Tuni jami’an tsaro suka bazama don zakulo matasan da suka aikata wannna aika-aika don ganin sun fuskanci hukunci.