An kashe mai unguwa an yi wa mai gadi yankan rago a Katsina

An kashe mutum 5 a gidan mai unguwa, aka sace mata da dama a a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia

An kashe mai unguwa an yi wa mai gadi yankan rago a Katsina

’Yan bindiga sun kashe mai unguwa da dansa da wasu mutun takwas a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.

A daren Laraba ne ’yan bindigar suka yi wa mutanen kisan gilla, ciki har wani mai gadi da suka yi wa yankan rago.

Wani dan yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce, zugar ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na dare, inda “suka kashe mai unguwa Magaji Haruna da dansa Idris, tare da wasu mutane uku a gidansa.

“Sun kuma shiga wani kamfani mai suna Tinna Tech inda suka yi wa wani mai gadi yankan rago, dayan kuma suka harbe shi har lahira, sannan suka cinna wa manyan motoci biyu da wata karama wuta.”

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun yi awon gaba da mata dama, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Shaidan ya ce tun da misalin karfe 5 na yammacin ranar aka fara fargabar yiwuwar kawo hari, sakamakon ganin ’yan ta’adda a kusa da kauyukna Taka-Tsaba da Yargeza.

Ya ce, saboda haka aka sanar da jami’an tsaro abin da ke faruwa, amma kuma a karshe da ’yan bindigar suka kawo farmakin babu wani mataki da suka dauka na dakile harin.

“Duk da cewa jami’an tsaro sun ba mu tabbacin cewa akwai karin jami’ai da za su turo idan har akwai barazanar hari, amma haka ’yan bindigar suka zo suka shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka, jami’an tsaro sun zo ba.

“Sai da ’yan bindigar suka gama barnarsu suka tafi sannan wata motar jami’an tsaro kwaya daya ta zo,” in ji shi.

Mazauna yankunan dai na zargin gaggan jagororin ’yan ta’adda Dankarami da Dangote ne ke aiwatar da hare-haren da ake fama da su a Karamar Hukumar Jibia da kewaye.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda