An kashe mai unguwa da wasu a kusa da Chibok

Wasu ‘yan Boko Haram sun kashe mai unguwan gari tare da wasu jama’a kusada garin Chibok dake jihar Borno kamar yadda ‘yan bangar unguwar suka sanar. Majiyar ta ce mayakan Boko Haram sun shiga garin ne a ababen hawa wasu a Babura. Garin dai ya kai nisan kilomita bakwai daga Chibok dake kudancin Borno inda […]

An kashe mai unguwa da wasu a kusa da Chibok

Wasu ‘yan Boko Haram sun kashe mai unguwan gari tare da wasu jama’a kusada garin Chibok dake jihar Borno kamar yadda ‘yan bangar unguwar suka sanar.

Majiyar ta ce mayakan Boko Haram sun shiga garin ne a ababen hawa wasu a Babura. Garin dai ya kai nisan kilomita bakwai daga Chibok dake kudancin Borno inda aka sace ‘yan mata 264  a watan Afrilu 2014.

Maharan dai sun kai 50 kuma sun shiga garin ne da misalin karfe 7:30 na dare.