Yadda aka kashe majinyata da ma’aikatan lafiya a asibiti a Filato
An bindige bindige jami’an tsaro da fararen hula tare da saran wasu da dama da adduna da harbin bindiga
Jana’izar mutanen da aka kashe a harin kauyen Kawel da ke Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato
Majinyata da ma’aikatan asibiti da jami’an tsaro na daga cikin mutane 22 da aka yi wa kisan gilla a wani mummunan hari da aka kai a yankin Kawel da ke Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.
Wani jami’in Kungiyar Agaji ta Red Cross da ke cikin wadanda suka yi aikin ceto bayan harin, ya ce maharan sun kashe ma’aikatan lafiya da marasa lafiya da suka iske a a Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko da ke kauyen.
Wani jami’in tsaro ya ce maharan sun kuma bindige jami’an tsaro da al’ummar garin tare da jikkata wasau da dama da saran adduna da harbin bindiga.
“An kai wadanda abin ya shafa asibiti domin jinyar su, wadanda raunkansu suka yi tsanani kuma an wuce da su jinya a wasu asibitoci a kananan hukumomin Mango da Bokkos,” a cewarsa.
- Tashin abin fashewa ya jikkata mutum ɗaya a Lagas
- An kama ɗan kasuwa yana sayar da gurɓatacciyar madara a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Me ya sa mutane suka dawo daga rakiyar Kirifto?
Ya kara da cewa an kona gidaje da rumubunan abinci da dama a yayin harin da aka kai a ranar Lahadi da dare, lamarin da ya tilasta al’ummar kauyen Kawel sun tsere zuwa wasu wurare domin samun mafaka.
Aminiya ta ruwaito Shugaban Matasan Bokkos, Christopher Luka, a safiyar Litinin yana an kai harin ne a da misalin karfe 11 na dare yayin da al’ummar kauyen suke barci a ranar Lahdai.
Luka shaida ya roki gwamnati ta dauki tsattsauran mataki a kan lamarin domin hana aukuwar irin harin, wanda aka kai ba tare da wani dalili ba, ko kuma bazuwarsa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa sabon harin ya zo ne kasa da kwana biyar da aka yi wa Dagacin yankin Gwande da ke Karamar Hukumar, Saf Samuel Alaket, kisan gilla a kusa da yankin Daffo a yayin da yake hanyarsa ta komawa gida bayan halartar wani taron sarakunan gargajiya.
Luka ya ce ya sanar da jami’an tsaro game da lamarin kuma a lokacin sun sanar da cewa cewa suna kan hanyarsu ta zuwa yankin.
Ya ce, “Na je yankin na ga yanayin abin da ya faru. Zuwa yanzu mutum 22 ne suka rasu, ciki har da mata.”
Gwamnatin Jihar Filato ta yi tir da harin tana mai bayyana shi a matsayin abin kyama mara dalili.
Sanarwar da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Joyce Ramnap, ya fitar ta ce Gwamna Caleb Mutfwang ya ba wa jami’an tsaro su tsaurara ayyukansu tare da kamowa da kuma hukunta masu hanni a kazamin harin.
Gwamnatin ta kuma ba wa hukumomin agaji umarnin bayar da tallafi ga mutanen da abin ya shafa tare da kira ga al’umma da su kwantar da hankali, su ba wa jami’an tsaro hadin kai tare da guje wa harin daukar fansa.