An kashe makiyaya uku a sabon hari a Filato

Ƙungiyar Matasan Berom (BYM) ta musanta zargin da MACBAN ta yi na cewa wasu ’yan ƙabilar Berom ne suka kai harin.

An kashe makiyaya uku a sabon hari a Filato

Aƙalla makiyaya uku aka kashe, yayin da wasu biyu suka jikkata bayan da wasu ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna a yankin Tanjol da ke Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Wani jagoran matasa a yankin, Abdullahi Ibrahim Yusuf, ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi yayin da makiyayan ke kiwo, inda har aka kashe saniya guda kuma aka raunata wata.

Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa babu dalili aukuwar irin wannan hare-haren.

Ya kuma yi kira ga makiyaya su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da buƙatar hukumomin tsaro su binciki lamarin domin hukunta masu hannu a ciki.

Sai dai Ƙungiyar Matasan Berom (BYM) ta musanta zargin da MACBAN ta yi na cewa wasu ’yan ƙabilar Berom ne suka kai harin.

Ƙungiyar ta ce waɗanda aka kashe na cikin waɗanda suka kai hari yankin Jol, amma jami’an tsaron sa-kai suka daƙile harin.

A cewar BYM, mutum guda mai suna Thomas Damang mai shekara 48 ya rasa ransa a harin, yayin da wasu uku suka jikkata.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar da rundunar Operation Enduring Peace ba su ce komai kan lamarin ba.

HOTUNA: An kama mutane 6 masu yi wa ’yan ta’adda safarar kayan masarufi a Borno

Shugaban Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS

Girgizar ƙasa ta yi ajalin mutum 6 a Peru

Mutum 6 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa