An kashe makiyayi da shanu 13 a wani sabon hari a Filato

Ƙungiyar ta roƙi gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

An kashe makiyayi da shanu 13 a wani sabon hari a Filato

Wani matashin makiyayi mai suna Sadi Aliyu, mai shekaru 15, ya rasa ransa bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari yankin Sabon Gidan Kanar da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta MACBAN a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo ne, ya tabbatar da faruwar harin.

A cewarsa, harin ya faru ne yayin da Sadi Aliyu da wasu makiyaya ke kiwon shanunsu, inda wasu ɗauke da makamai suka afka musu tare da buɗe musu wuta.

Ya ce matashin makiyayin ya mutu nan take, yayin da shanu 13 suka mutu sakamakon harin.

Haka kuma, har yanzu ana neman wasu shanu 11 da suka ɓace bayan aukuwar harin.

Babayo, ya yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya ce an kai rahoton lamarin ga rundunar ’yan sanda da kuma jami’an Operation Enduring Peace.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da roƙon makiyaya da su kwantar da hankalinsu su bar hukumomin tsaro su gudanar da aikinsu.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an Operation Enduring Peace ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.