An kashe malamin addini da manoma 5, an sace mutum 40 a Birnin Gwari

An kashe mutanen ne a gonakinsu suna tsaka da aiki

An kashe malamin addini da manoma 5, an sace mutum 40 a Birnin Gwari

‘Yan Bindiga

’Yan bindiga sun kashe manoma shida, cikinsu har da Mataimakin Shugaban kungiyar Izala na Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, Malam Yakubu Bugai.

Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kuma sace sama da mutum 40 lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a yankin mai fama da hare-hare.

Shugaban Kungiyar Ci Gaban Masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Kasai ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce an kai farmakin ne ranar Larabar da ta gabata.

Ya ce an kashe malamin addinin ne a gonarsa da ke kusa da kauyen Rema, daga bisani aka dauki gawarsa aka kai asibitin Jibril Mai-Gwari da ke Birnin Gwari.

Ishaq ya ce an harbi malamin a cikinsa da kuma a kafadarsa.

Sai dai ya ce malamin ya riga mu gidan gaskiya wajen misalin ƙarfe 7:30 na yammacin Alhamis.

“Kafin rasuwarsa, Malam Yakubu Bugai babban jigo ne a yankin, kuma wanda ya kafa gidauniyar kula da marayu ta Birnin Gwari, wacce ta sadaukar da kanta wajen kula da dubban marayun da suka rasa iyayensu galibi sakamakon matsalar tsaron yankin,” in ji sanarwar.

Bugu da kari, sanarwar ta ce an kuma yi awon gaba da sama da mutum 40 a dajin Kuyambana, wanda dama bata-garin ke amfani da shi a matsayin maboya.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele