An kashe manoma 18 a sabon hari a Filato
An kai harin ne a yayin da mazauna kauyen suke barci a ranar Lahdai da misalin karfe 11 na dare.
Akalla maonma 18 ne aka kashe, tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da aka kai a daren Lahadi a kauyen Kawel da ke gundumar Mushere a Karamar Hukumar Bokko ta Jihar Filato.
Shugaban Matasan Bokkos, Christopher Luka, ya shaida wa Aminiya a safiyar Litinin cewa an kai harin ne a yayin da mazauna kauyen suke barci a ranar Lahdai da misalin karfe 11 na dare.
Luka shaida wa wakilinmu cewa wani dan kungiyar ne ya sanar da shi game da sbon harin da aka kai a cikin dare.
Ya ce, “Wani shugaban matasa ne ya kira ne da misalin karfe 12 na dare cewa ’yan bindiga sun kawo hari tare da harbe mutane sama da 20, kuma an tabbatar da mutuwar 18 daga cikinsu.”
- An kona matar aure da ranta kan zargin satar yara a Kaduna
- Bello Turji ya ɗauki alhakin kashe sojoji a Sakkwato
Wakilinmu ya ruwaito cewa sabon harin ya zo ne kasa da kwana biyar da aka yi wa Dagacin yankin Gwande da ke Karamar Hukumar, Saf Samuel Alaket, kisan gilla a kusa da yankin Daffo a yayin da yake hanyarsa ta komawa gida bayan halartar wani taron sarakunan gargajiya.
Luka ya ce ya sanar da jami’an tsaro game da lamarin kuma a lokacin sun sanar da cewa cewa suna kan hanyarsu ta zuwa yankin.
Ya bayyana harin a matsayin mara dalili yana mai kira ga jami’an tarso da su dauki tsattsauran mataki wajen shawo kan matsalar tare da hana bazuwarsa.
Zuwa lokacin da muka samu wannan rahoton, jami’an tsaro ba su yi magana kan lamarin ba. Wakilinmu yakira kakakin ’yan sandna jihar Filato, SP Alabo Afred da kuma kakakin rundunar sojoji ta Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Auta, amma har muka kammala wannan rahoton ba su amsa sakon wakilinmu na neman karin bayani ba.