An kashe manoma 7, an ƙone buhun masara 50 a Neja
Maharan sun kuma kashe wani mutum bayan karɓar miliyan 20 kuɗin fansa daga hannun iyalansa.
Aƙalla manoma bakwai, ciki har da wani ɗan agaji, ’yan bindiga suka kashe, tare da ƙone buhun masara 50 a garin Bangi da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a Jihar Neja.
Shaidu sun ce manoman suna kan hanyar dawowa daga gonakinsu da motar da ta ɗauko masara, maharan suka yi musu kwanton ɓauna.
- Na yi wa mahaifina alƙawarin ba zan taɓa aikata masha’a ba — Murja
- DSS ta kama jami’in hukumar agaji na bogi
Sun kashe duk wanda ke cikin motar sannan suka ƙone motar tare da masarar.
Wani ganau ya ce, “’Yan bindigar sun jira har sai da manoman suka gama loda buhun masara 50 a cikin motar.
“Suna barin gonar, sai suka buɗe musu wuta, suka kashe su sannan suka ƙone motar tare da masarar.”
Manoma a Mariga suna shan wahala wajen girbin amfanin gonarsu, saboda hare-hare, kashe-kashe da satar mutane da ’yan bindiga ke yi a yankin.
A wani lamari kuma, ’yan ta’adda sun kashe wani mazaunin garin Kontagora, Malam Danjuma duk da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 20 daga hannun iyalansa.
Danjuma ya shafe makonni uku a hannun maharan kafin su kashe shi.
Wani mutum da ya tsere daga hannun ‘yan bindigar ya sanar wa iyalan Danjuma labarin mutuwarsa.
Yahaya Suleiman, wani mazaunin Kontagora, ya ce garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu sassan garin a ’yan makonnin nan.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kashe manoman bakwai.
Ya ce, “A ranar 16 ga watan Nuwamba, da misalin ƙarfe 3 na rana, an yi wa mutum bakwai kwaton ɓauna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikinsu.”
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da sojoji sun tura tawagarsu zuwa yankin don hana sake faruwar lamarin.