An kashe masu aikin Polio 7 a Pakistan
‘Yan sandan kasar Pakistan sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’ansu bakwai da ke kula da masu yin allurar rigakafin cutar shan inna a birnin Karachi shekaranjiya Laraba.Sun ce an kashe ‘yan sandan ne a hare-hare biyu daban-daban da aka kai musu.Sai dai harin bai shafi masu aikin allurar foliyon ba.Wadannan dai su ne […]
‘Yan sandan kasar Pakistan sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’ansu bakwai da ke kula da masu yin allurar rigakafin cutar shan inna a birnin Karachi shekaranjiya Laraba.
Sun ce an kashe ‘yan sandan ne a hare-hare biyu daban-daban da aka kai musu.
Sai dai harin bai shafi masu aikin allurar foliyon ba.
Wadannan dai su ne hare-hare na baya bayan nan da ake kai wa masu bayar da allurar rigakafin polio a kasar.
Pakistan na cikin kasashe biyu da suka rage a duniya da ke fama da cutar ta shan inna.
Masu kai hare-hare na yin tarnaki wajen ganin an kawar da cutar a kasar.
Masu tsananin kishin Islama suna adawa da rigakafin, inda suke cewa wani makarkashiya ce da kasashen Yamma suka shirya don hana al’ummar Musulmi haihuwa.
A watan Janairun da ya gabata, akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu bayan wani bam da aka dasa a birnin kuetta da ke Kudu-masu-Yammacin kasar.