An kashe masu garkuwa da mutane 4 a hanyar Abuja zuwa Lokoja

‘Yan bangan kauyen Manyare da ke kusa da birnin Kotonkarfe a hanyar Abuja zuwa Lokoja sun harbe wasu mutum hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, uku daga cikin wadanda ake zargin  masu garkuwa da mutane ne ann kama su lokacin da suke kokarin tserewa cikin daji. Wani […]

An kashe masu garkuwa da mutane 4 a hanyar Abuja zuwa Lokoja

‘Yan bangan kauyen Manyare da ke kusa da birnin Kotonkarfe a hanyar Abuja zuwa Lokoja sun harbe wasu mutum hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, uku daga cikin wadanda ake zargin  masu garkuwa da mutane ne ann kama su lokacin da suke kokarin tserewa cikin daji.

Wani daga cikin ‘yan bangar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce sun harbe masu garkuwan da mutanen ne a safiyar yau Talata da misalin karfe 6:37 lokacin da suke farautar ‘yan bindigar.