An kashe matafiya biyar a Adamawa
Hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kisan wasu matafiya biyar a kauyen Pasham dake hanyar Jalingo a karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa. Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar, ya ce wasu ake zargin ‘yan banga a garin ne suka kashe matafiyan tare da raunata bakwai. A yanzu haka ana ci […]
Hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kisan wasu matafiya biyar a kauyen Pasham dake hanyar Jalingo a karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa.
Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar, ya ce wasu ake zargin ‘yan banga a garin ne suka kashe matafiyan tare da raunata bakwai. A yanzu haka ana ci gaba binciken wadanda suka aikata wannan laifin.
Othman ya bukaci mazauna unguwar da su kwantar da hankulansu cewa, jami’an tsaron na yin bakin qoqarinsu na tsaron jama’a da dukiyoyinsu.